Daga Idris Aliyu Daudawa, Abuja
Sanata Enyinnaya Abaribe mai wakiltar mazaɓar Abiya ta Kudu a Majalisar Dattawa na fuskantar matsaloli, waɗanda suka shafi Nnamdi Kanu. A matsayinshi na wanda ya tsaya wa Kanun lokacin da za a bayar da belin shi.
Gwamnatin Tarayya ta ba Abaribe amsar wata takarda da ya rubuta, wacce a cikinta ya nemi da a cire shi daga cikin jerin waɗanda suka tsaya wa Kanu. Inda gwamnatin ta ce, wannan zancen kawai ne, marar muhalli.
A takardar ɗaukaka ƙarar da gwamnatin tarayyar ta gabatar ga Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta sanar da Sanatan cewa, Kanu na hannunsa, kuma babu makawa sai ya fito da shi, don a ci gaba da sauraron shari’arsa.
Don haka, gwamanatin tarayya ta ƙalubalanci Sanata Abaribe da cewar ko yana da masaniyar Kanu ya karya sharuɗɗan belin da aka gindaya masa, waɗanda ita Kotu mai alfarma ta gindaya kafin ta amince da bayar da belin shi, ranar 24 ga Afrilu, kafin 11 ga Satumba lokacin da ya ce, shi bai san halin da wanda ya amshi belin shi ke ciki ba, saboda basu magana.
Ita dai takardar rantsuwar ga ta kamar haka ‘’ An dai ƙarya alƙawari wanda kuma an saɓa ma sharuɗɗan amsar Beli, kuma yakamata shi Sanatan ya kawo wanda yai Beli, ko kuma ya kawo takardar neman haka, idan ba haka ba to abin ya zama wasan yara kenan.
Mai neman haka kamata yai tuni ya sanar da kotun cewar shi wanda za a gurfanar da shi a gaban kotu domin cigaba da shari’ar, ya karya sharuɗɗan da suka kamata, bai kawo kanshi ba kotu, wannan ai ba ƙaramin laifi ba ne.
Mai gabatar da masu laifi Mr Sha’aibu Labaran ya nuna rashin jin daɗinshi cewar Abaribe bai ƙyauta ba, saboda ya taimakawa mai laifi, wato Kanu shine ya karya sharuɗɗan Beli, ya ce, Kanu baya hannun soja, ita kuwa gwamnatin tarayya cewa ta yi Kanu yana tare da Abaribe. Amma Abaribe bai yarda da cear ya san wurin da Kanu yake. Ya ce, bai san wurin da Kanu yake ba, amsar wannan tambaya zata iya samuwa ne kawai idan aka zauna kan sauraren ƙarar.
Kanu bai bayyana a Kotu ba ranar 17 ga watan Oktoba, amma kuma wani mabu mai ɗaure kai shine, waɗanda yakamata a saurari ƙarar tasu tare, su an kawo su kotu wanda kuma, ma’aikatan gidan yari ne suka kawo su.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Litinin ne ta tsaida 14 ga watan Nuamba za a cigaba da sauraren ƙarar da shi shugaban masu fafutukar samar da ƙasar Biyafara ya shigar, inda yake son ya san dalilin da suka sa aka soke rajistar ita ƙungiyar ta samu.
Ita dai ƙarar da an faɗi ranar da za a sake zaman saurarenta ne amma wadda mai shari’a Abdu Kafarani ke shugabanta, ranar Laraba amma shi mai shari’ar baya nan, ya tafi wurin yin wani taron ƙara wa juna ilmi, a cikin Abuja.
Ƙungiyar fafutukar neman ƙasar Biyafara ranar 22 ga Satumba ta shigar da ƙara inda take buƙatar, da janye ita maganar soke ƙungiyar, da kuma ɗaukarta a matsayin ƙungiya ta ‘yan ta’adda.