Abba Ibrahim Wada" />

Martial Da Rashford Za Su Fara Kokari— In Ji Barbatov

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Dimiter Barbatov ya bayyana cewa matasan ‘yan wasan kungiyar guda biyu, Anthony Martial da Marcus Rashford za su haskaka a wannan shekarar duk da cewa suna shan suka daga bangaren magoya bayan kungiyar.

Duk ‘yan wasan guda biyu dai basa samun buga wasa akai-akai bayan da Mourinho yafi amfani da Lukaku da Alexis Sanches tun bayan da Sanches din yakoma kungiyar a watan Janairun daya gabata.

Rashin buga wasanne ne yasa dan wasa Martial bai samu wakiltar kasarsa ta Faransa ba a gasar cin kofin duniya kuma kasar ta Faransa taje ta lashe kofin bayan ta doke kasar Croatia a wasan karshe.

Sai dai Rashford ya wakilci kasarsa ta Ingila kuma ya buga wasanni a wasannin da kasar ta buga a gasar cin kofin duniya a rasha inda kasar ta Ingila takai wasan kusa dana karshe sannan kuma tayi na hudu a gasar.

Barbatov yace, matasan ‘yan wasa ne wadanda kuma nan gaba kadan tauraruwarsu zata haska a duniya saboda haka dole sai anyi hakuri dasu da kuma irin abinda zasu dinga bugawa a fili.

Ya ci gaba da cewa amma idan suka samu damar bayyanawa duniya kansu za’ayi mamaki kuma zasuyi tsada a duniya idan kungiyar taga zata iya siyar dasu.

Martial dai ya bayyanawa Manchester United cewa yanason barin kungiyar bayan ya dayaga baya samun buga wasanni.

Exit mobile version