Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester united, Anthony Martial, wanda kuma ya ci wa ƙungiyar ƙwallonta ɗaya tilo data doke Tottenham a ranar Asabar ɗin data gabata ya ce, shi ba ɗan benci bane kuma baya son zama a benci.
Ɗan wasan yashigo daga baya saura minti 20 a tashi daga wasan bayan yayi canjin Marcus Rashford daga wasan kuma yasamu nasarar jefa ƙwallon a daidai minti na 81 da fara wasa.
Ƙwallon da ya ci ita ce ƙwallo ta hudu da ɗan wasan yaci idan yashigo wasa daga baya wato a ƙarshen wasa sai dai ɗan wasan ya bayyana cewa shima nan gaba zai samu cikakken lokaci.
“Mourinho ya gayamin cewa in koma gefe in tsaya domin za a yi amfani da Lukaku a jefa masa ball shi kuma zai gyaramin da kansa kuma hakan akayi muka samu nasara”inji Martial.
Martial dai a wasannin da ya buga a ƙungiyar wanda aka fara dashi a farkon lokaci bai zura ƙwallo a raga ba duka ƙwallayen da ya zura sai idan yashigo daga baya.