Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta shirya taron ne, don dakile da kawar da fyade a Jihar Katsina karkashin kungiyar Al’ummah ‘Support and Initiative’ da hadin gwiwar Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu na jihar.
Jihar Katsina ta zama kan gaba a yawaitar yi wa mata fyade na manya da kananan yara a arewacin Najeriya. Abin da ke ci ma mahukunta da duk wani wanda yake da ruwa da tsaki a jihar tuwo a kwarya. Gwamnatin Jihar ta Katsina karkashin jagorancin Gwamna Rt Hon Aminu Bello Masari ta damu kwarai har ya kasance ta zama jaha ta farko wajen sa hannu a kan doka ga duk wanda aka samu da wannan mummunan laifin na fyade.
Ganin irin wannan matsaloli ya sa kungiyar Al’umma Support Initiave ta yunkura tare da yin gangamin hada taro tare da hadin gwiwar ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jahar Katsina karkashin kwamishinanta, inda aka yi taro, don wayar da kan mata kan yawaitar fyade tare da kawo hanyoyin dakile shi a Jihar Katsina karkashin jagorancin kwararriyar marubuciyar nan, Dr. Bilkisu Yusuf Ali.
Taron da aka yi ranar Alhamis 7 ga Janairu a shekarar 2021 a dakin taro na Multi-Purpose center Filin Samji ya tattaro muhimman batutuwa da hanyoyin dakile Fyade a jahar. A jawabin kwamishinan Kananann hukumomi da masarautu, Rt Hon Alh Ya’u Umar Gwajogwajo, ya fara da godewa Allah da maigirma gwamna kan bayar da dukkan tallafin da ya dace domin gudanar da wannan taron sannan ya ce gwamnati a shirye take don daukar nauyin wannan taron a duk fadin kananan hukumomin jihar Katsina don haka yana rokon wadda ta yi wannan tunani na kirkirar wannan taro Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali don fadada wannan taron a sauran kananan hukumomin jihar.
A karshe ya yi addua kan masu aikata wannan masifa Allah ya ganar da su in jarrabace in kuma wani neman abin duniya ne Allah ya shiryar da su. Ya kuma roki masu halin cikinmu da su fito su taimaka da sauran jama’a kowa yasan halin da ake ciki a yanzu matasa a samar musu da aikin yi.
Haka mata a samar musu da abin yi a cikin gidajensu na sana’oi wanda hakan ne zai rage tallace-tallace da ake dorawa ‘ya’ya mata. Ya yi kira da Iyaye da za su gane wannan kayan dakin da gara da hidimar bikin da ake yi ana kashe makudan kudade da iyaye za su gane da sun tattara kudin su ba wa ‘yarsu ta ja jari ko su saya mata abin sana’a. sannan a dukkan bangarorin biyu a samar da hanya ta saukaka aure.
Malamai su ci gaba da wa’azantarwa. Ya nuna debe kunya da mutane suka yi a idanuwansu bala’i ne. A da mutum idan ya yi abin kunya barin gari yake amma ban da yanzu sai a a kama mutum da irin wannan laifin amma ka ji yana mai da magana ko yana musu idonsa kir!Al’umma ya kamata mu dawo kan ka’ida mu ga in Allah bai kawo mana dauki ba. Lallai mai girma gwamna yana cikin bacin rai kan abin da yake faruwa na fyaden ‘ya’ya mata da sauran Abubuwa.”
A nata jawabin Kwamishiniyar Mata ta jahar Katsina Hajiya Rabi’a Mamman Daura ta ce a fyade ba iya ‘ya’ya mata kawai ake yi wa ba a wannan lokacin har da ‘yaya maza kuma abin takaicin an kasa gano musabbabin a yanzu. Makarantun boko da ma makarantun allo abin takaici har da su ake samun wannan matsalolin.
Nauyin kawar da wannan na kan iyaye mata har da iyaye maza. Ya kamata duk a sa ido akan shige da ficen yaranmu. Haka masu unguwanni da dattijan unguwa. Mun yaba kwarai da kokarin wannan kungiya don kuwa duk abin da ya shafi mace ya shafi al’umma ne . Sannan duk inda za a gabatar da wannan taron ko bita za mu bi kuma mu bayar da gudummawa. Ma’aikatar mata muna nan muna ta kokarin mu ga mai za mu yi ma mata a wannan sabuwar shekara da muke ciki. Bara annonar korona ta zo ta hana mu abubuwa da dama amma bana kam da yardar Allah mata za su dara. Ina yi wa kowa barka da zuwa da fatan alheri.
Mai ba wa gwamna shawara akan ilimin ‘ya’ya mata Hajiya Amina Lawan Dauda harkokin mata ta Jihar Katsina ita kuwa ta fara jinjina ne ga kokarin da aka yi na shirya wannan taro wadda shugabar kungiya Hajiya Bilkisu Yusuf Ali ta yi inda ta nuna wannan taron shi ne irinsa na farko a jihar Katsina don haka ta kira wannan rana da rana mai albarka, rana mai matukar muhimmanci don taro ne na jawo hankali wanda aka bata lokaci ana shirya shi don a ga ya tabbata kuma ya yi inganci.
Batun Fyade abu ne mai tayar da hankali , annoba ce wadda ba ma a gane kan masifar. A da ‘yan mata ake yi wa fyade amma a yau abin takaici ne don ba ma a iya gane dalilin wannan masifa babu mai cewa ga hujja a wani lokacin a yi wa tsohuwa shekara saba’in ko yarinya ‘yar wata uku, kwanan nan ma an kawo yarinya yar shekara uku wanda wanda ya yi mata fyaden wani mutum ne da aka taimakawa da matsugunni a gidan su yarinyar baban ya taimaka masa.
Don wasu matan akan same su cutoci da ake dauka kamar HIB da ciwon Sanyi da Hapatatis da sauransu bayan an yi musu fyade. Akwai wani kokari da muke yi karkashin ofishina za mu bude wajen gwaje-gwaje mu sami lauyoyi da za mu bi wannan laifin na fyade har a zartar da hukunci. Akwai doka za ta fito karancin dokar in an yi fyaden daurin shekara 27 in kuma mutuwa ta gitta daurin rai da rai, amma mu mata muna so a kashe ne. ofishina zai taimaka da yaki da fyade dari bisa dari.
A jawabin da kakakin ‘yansanda ta jahar Katsina SP Gambo Isah ya yi bayani mai taba zuciya na yadda matsalar fyade ke ruruwa a jahar. Ya bayyana laifukan fyade da aka fi samu a jihar Katsina kashi casa’in akan kananan yara ne daga uku zuwa shekara sha hudu. Kuma sun fantsama ko’ina cikin jihar birni da kauye. A shekarar da ta gabata an kama mutane dari da tamanin da bakwai. SP ya ci gaba da bayyana abubuwan da kan janyo fyade ciki kuwa har da rashin tsaro.
A batun hukunci kuwa SP ya bayyana hukuncin fyade da daurin rai da rai ko kuma hukuncin kisa idan yakasance lokacin da yake aikata laifin an samu mutuwa sashe na 254KT PC, wanda aka kama da laifin yin luwadi kuwa shima za a hukunta shi da daurin rai da rai (Sashe 255 KT PC).
SP Gambo Ya bayyana namijin kokarin da jami’an tsaro ke yi na kamawa da kai wa ga hukuma na duk aka samu da laifin fyade sannan ya yi roko ga iyaye kan duk wadda tsautsayin fyade ya afka mata kada a wanke ko a gyarata a dauketa a kai ta ga hukuma a yananyin da aka same ta, ta haka ne za a iya yin bincike a asibiti har a gano mai laifi.
Ya bayyana jin zafinsa na yadda za su ga ga mai laifi dukkan alamu sun nuna amma suna ji suna gani dole su sake shi saboda rashin shaida. A karshe ya rufe da shawarwari har guda goma sha shida wadanda shakka babu in an bi su za a dakile yawaitar fyade a jihar Katsina.
A jawabin wadda ta shirya taron Hajiya Bilkisu Yusuf Ali ta bayyana makasudin shirya wannan taron shi ne yadda za a kawo hanyoyin da za a dakile fyade a jihar Katsina. Kuma kamar yadda jawabai suka gabata to tabbas wannan taro kwalliya za ta biya kudin sabulu don taron na yau ya bambanta da sauran tarurruka da aka saba yi.
A takardar kuwa da ta gabatar mai suna Hannu daya ba ya daukar jinka: Kawar da fyade a jahar Katsina Hajiya Bilkisu Yusuf Ali ta kawo illolin da fyade kan janyo kama daga kan lafiyar jiki da kwakwalwa da kuma gangar jiki. Sannan ta kawo hanyoyi da ya kamata a bi don magance yawaitar fyade a jihar Katsina. Wannan taro ne wani dan ba ne aka saka har sai an tabbatar fyade ya zama tarihi a jihar Katsina da ma sauran jihohin Arewa gaba ki daya.
Hajiya Bilkisu ta gode wa duk mahalarta taron bayan sun gabatar da tambayoyinsu da tsokacinsu gareta kuma ta ba su amsa a sashen tambaya da amsa.
Taron ya sami halartar matan shugabannin riko na kananan hukumomin jihar Katsina da shugabannin mata da shugabannin kungiyoyin da’awa na mata a kananan hukumomi.