Marubutan Batsa Ku Ji Tsoron Allah -Emili
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Marubutan Batsa Ku Ji Tsoron Allah -Emili

byAdamu Yusuf Indabo
6 months ago
Batsa

Fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, ‘yar asalin Zinder da ke Jamhuriyar Nijar, wacce aka fi sani da Emilia. Ta yi wannan kira ne ga ‘yan uwanta marubuta da su sanya tsoron Allah a cikin rubuce-rubucensu musamman ma dai marubutan batsa, wadanda ta ce suna warware tufkar da sauran managartan marubuta ke tufkawa da badalar da suke yada wa duniya. Marubuciya Emilia dai ta yi wannan kira ne a yayin tattaunawarta da wakilin LEADERSHIP Hausa, wato Adamu Yusuf Indabo. Ga dai cikakkiyar tattaunawar tasu kamar haka:

To farko mene ne cikakken sunanki, da kuma takaitaccen tarihin rayuwarki?

  • Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano
  • Bukatar Kawo Karshen Mamayar Da Kamaru Ke Yi Wa Yankunan Nijeriya

Sunana Zouley Sabitou. An haife ni 23 ga watan Afrilu a shekara 2003 a garin Yékoua ce da ke jahar Zinder/Damagram, na yi nursery a garin Arlit da kuma aji biyu na primary, na yi sauran primary da secondry a garin Agadez da kuma karatun addini duk a nan Agadez, ina Unibersity ne a garin Dosso. Enbironnement et numérikue nake karantawa a Unibersity duk da dai na yi karatun likitanci yanzu kam sai na koma harkar gonaki da muhalli.

To sunan Emilia da kowa ya san ki da shi, ina ya samo asali?

Sunan zouleyha kakana ne ya saka min shi to daga baya mahaifina ya canza min suna yana kira na ne da Émilia har kuma sunan ya bi ni wanda har Zouley din kan yi nisan kiwo.

To mun san ki a matsayin marubuciyar littafan Hausa. Shin ta ya kika tsinci kanki a duniyar rubutu?

Hukuncin Ubangiji, na yi karance-karance da dama a baya, tun ina karamar secondary na fara rubuta labari a paper a shekarar 2016, idan na rubuta sai na ajiye. Lokacin da muka yi hutu da aka dawo aji na Hudu (a kasar Nijar shekara 4 muke yi a karamar secondary) a karamar secondary a lokacin na fara karantawa kawayena, idan an yi break, to bayan na gama karama secondry na ci gaba da rubutun a paper, a shekara ta 2019 na fara rubutu a yanar gizo har na fara yadawa.

A 2016 mene sunan littafin da kika fara rubutawa?

Gaskiya ba zan iya tunawa ba, don a lokacin ban wani kware a rubutu ba, bayan na gama karanta musu na kan nemi shawararsu a kan yadda labarin zai ci gaba ko abin da ya dace na canza ko sunan da ya dace da labarin.

To wanda kin fara yadawa a yanar gizo cikin shekaran 2019, wanne littafi ne?

Khairat: sunan littafin da na fara fitarwa a 2019 shi ne KHAIRAT. Labarin ya ginu ne don jan kunne ga irin iyayen da suke nacewa sai ‘ƴarsu ta yi karatu kuma a kasashen waje, sai a yi rashin sa’a ita kuwa yarinyar aure take son yi, daga nan rayuwar yaran za ta iya lalacewa, duk da ita Khairat din a nata bangaren ta yi aure ne a boye ba tare da sanin iyayenta ba a kasar da suka aika ta karatu. To bayan Khairat kuma zuwa yanzu na yi wasu littafan guda (14) har da shi ya zama ina da littafai (15) ke nan da na fitar, kuma dukkansu a yanar gizo. Littafan guda Goma Sha Biyar kuwa su ne: Khairat, Nazi’at, Na Yi Asara, Babbar ‘Yar Duniya, Dan Kuka, Mutuwar Aure, Samha, Tura Ta Kai Bango, Gudun Tsira, Dambarwar Aurensu, Dambarwar Abin Dake Raina, Kuskure, Da Wata Kusan, Abin Dake Boye, Kwakwalwar Kifi.

A cikin wadannan littafai guda 15, wanne ne bakandamiyarki?

Labarin ‘Kuskure’ shi ne bakandamiyata. Labari ne da aka gina shi a kan gudun son zuciya, cire kiyayyar wani mutum a rai saboda ba ka san abin da gobe za ta haifar ba. Don gaba da kiyayya ba su da amfani, kuma Manzon Rahama ma ya hane mu a kan zurfafawa a cikin kiyayya.

Kika ce a baya kin yi karance-karancen littafan Hausa. To cikin marubuta na wancan lokacin wace ce gwanarki?

To ai ni har yanzu ban daina karance-karancen Hausa ba. Duk da asalin marubutan sun daina rubutun zube, amma an samu sabbin marubuta. A da gwanata ita ce marubuciya Fauziyya D Sulaiman. A yanzu kuwa zabin tilo a cikin marubuta gare ni zabi ne mai wahala. Sai dai zan iya cewa: a bangaren zamantakewa marubuciya ‘Billyn Abdul’ ce gwanata, idan kuma bangaren horror sai na ce ‘Chamsiya Laouli Rabo’ idan kuma littafin yaki ne to marubuci ‘Mansur Usman Sufi’.

To ko cikin marubuta kina da kawa shakikiyar da kowanne lokaci za a iya samun labarin halin da keki ciki a wajenta?

Kwarai ina da Aunty Fa’iza Abubakar wadda aka fi sani da Maman Afrah.

To ya batun kungiyar marubuta?

Ina cikin kungiyar First Class Writer’s Association wadda tun farkon fara rubutuna antyna Rahama Sabo Usman ita ce ta saka ni a cikinta.

To a matsayinki na tsohuwar makaranciya, ya za ki kimanta marubutan da da kuma na yanzu ta fuskar kwarewa da ilimantarwa?

Babu hadi gaskiya domin kowa akwai matsayinsa, marubutan da sun yi rubutu ne a kan matsalolin da suka shafi al’umma a da, su kuwa marubutan yanzu suna rubutu ne a kan abin da ta shafe mu yanzu, duk da dai yanzu bin ka’idodi da dokokin da adabi ta tanadar ya yi karanci fiye da da can baya saboda yanzu duk wanda ya ga dama zai iya zama marubuci, sai kuma baragurbin marubuta wato marubutan batsa da suka yi yawa a halin yanzu wanda muna tufka su kuwa suna warware wa ne.

To ya batun shiga gasar rubutu?

A duk lokacin da zan ji labarin gasar rubutu bana kasa a guiwa wajen shiga, wasu an yi nasara wasu kuwa ba a yi ba, duk da dai iya shiga gasar ma nasara ce babba. Gasar da na yi nasara kuwa. Akwai gasar da aka shirya a lokacin bikin marubuci Yareema Shaheed gaskiya na manta sunan gidan tb da suka shirya gasar. Sai gasar da kungiyar raya al’adu ta jihar Gombe suka shirya.

Kuma a wanne yanayi ko lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?

A duk lokacin da na ci na koshi bana kuma tare da gajiya, sha’awar yin rubutun kan zo mini.

To wadanna nasarori kika cimma a rayuwa ta sanadiyyar rubutu?

Na farko babbar nasara ta ita ce haduwa da mutanen kirki wanda a halin yanzu suke tamkar ‘yan uwana kama daga marubuta har makaranta.

Nasara ta biyu kuma harkar rubutu na saka ni alfahari don a duk inda zan shiga bana jin shakkar kiran kaina da marubuciya. A yanzu kuma bayan fadakarwar da nake yi ina daukar harkar rubutu a matsayin hanyar da zan samu dan na kashewa saboda bunkasar tattalin arzikina.

To wanne kalubale kika fuskanta bayan shigowar ki duniyar rubutu?

Da farko dai kalubalen da na fuskata daga mahaifiyata ne don ina fama da matsalar ciwon ido a lokacin idan na zauna na fara rubutun a waya ko laptop, za ta rika faka a kan ba ki da lafiya amman kullum kina jone da wannan screen ɗin don yin rubuce-rubuce, amman daga baya da rashin lafiyar ya yi sauki sai kawai ta daina mita tana yi min fatan alkairi. Kalubale na gaba kuwa ina son makaranta su rika yi min comment a duk bayan da suka karanta labarina sai dai kuma ba sa yi sai an kai ruwa rana.

Ko wanne kira za ki yi ga ‘yan uwanki marubuta?

Kirana ba zai wuce mu ji tsoron Allah a duk sanda za mu kaura alkalami ba, mu rubuta abin da zai anfane mu ya anfani al’umma, abin da ko da an tambaye ki gobe ba za ki yi da-na-sanin rubuta shi ba, kuma abin da ko ‘ƴarki ko kawarki za ki iya bari ta karanta. Sannan mu rike zumunci da karfafa juna ta hanyar karawa juna sani a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, domin duk inda marubuci yake to fa dan uwanmu ne. Sai kuma marubutan batsa ku ji tsoron Allah.

To wanne sako kike da shi ga masoyanki da suke bibiyar rubuce-rubucenki?

Ina yi wa duk wani masoyina fatan alkairi, da fatan Allah Ya biya masa bukatunsa na alkairi kuma ina mai farin cikin sanar da su zan ci gaba da fadakar da su da kuma nishadantar da su gwargwadon iyawata.

To Hajiya Emilia muna godiya.

Ni ce da godiya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)
Adabi

Nazari Kan Littafin Baba Zube Na 5 (Gwamnati)

September 26, 2025
Dr. Maryam Yola Ta Zama Farfesa Mace Ta Farko Kan Magungunan Gargajiya Da Al’adun Hausa
Al'adu

Dr. Maryam Yola Ta Zama Farfesa Mace Ta Farko Kan Magungunan Gargajiya Da Al’adun Hausa

December 30, 2024
Farfesa Zaynab Alkali: Mace Ta Farko Da Ta Zama Marubuciyar Littattafai Daga Arewacin Nijeriya
Adabi

Farfesa Zaynab Alkali: Mace Ta Farko Da Ta Zama Marubuciyar Littattafai Daga Arewacin Nijeriya

November 23, 2024
Next Post
Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume

Ndume Ya Yaba wa Sojoji Kan Daƙile Harin Boko Haram A Gwoza

LABARAI MASU NASABA

An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version