Jamila Umar Tanko" />

‘Marubutan Kafar Sada Zumunta Na Durkusar Da Tasirin Rubutu’

Fagen rubutu wani sashe ne mai matukar muhimmanci ga sha’anin bunkasa zamantakewar al’umma a duk inda suke. Shi ya sa duk al’ummar da ta fahimci kanta ba ta yin sakaci da rubutu kasancewar yana da tasiri sosai wajen jan akalar rayuwar jama’a. Sai dai kuma ga dukkan alamu sashen yana fuskantar wata matsala da  bakuwarmu ta wannan makon ta ce tana durkusar da rubutu da marubuta. Matsalar kuwa it ace marubutan shafukan sada zumunta na zamani. To ko yaya abin yake? Malamar ta yi cikakken bayani a cikin firar:

Da wa muke tare…

Sunana Maryam Nuhu Turau Rafindadi.

Takaitaccen tarihi

An haife ni a Katsina a Unguwar Rafindadi, na yi furamare a Rafindadi na je Sakandare wadda a ka fi sani da WTC Katsina, na yi j.s. 1-3 sannan na koma ‘unity girls college’ Jibiya na ida SS1-3. Sannan na ziyarci makarantar horas da Malamai F.C.E Katsina na karanta Nazarin koyarwa a furamare da Hausa. Na yi makarantar Allo da ta Islamiyya na sauke Alkur’ani mai girma da kadan daga cikin wa su littattafan addini.

 

Littafanki nawa?

Na rubuta littafi guda biyu ‘Duniya Ta Yi Zafi’ da ‘So Nakasar Rayuwa’.

 

Ki bayyana wa masu karatu jigon littafan naki daya bayan daya da kuma irin sakon da kike son isarwa ga al’umma…

Jigon littafin Duniya ta yi zafi shi ne ‘Tsarin Iyali’, na yi kokarin nuna ma mutane yawan haihuwa ba ya kawo talauci kamar yadda wa su ke fadi, an wayi gari yau Bature ya kimsa mamu kin son haihuwa dan kauce ma talauci, sun manta cewa Allah shi ne mai azurta wanda ya so ba dan ya fi son shi ba, kuma shi ke talauta wanda ya so ba dan ba ya son shi ba. Ya na da kyau mutane su yi amfani da fadar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallama da ya ce “Ku yi aure ku hayayyafa dan in yi alfahari da ku ranar gobe kiyama”.

Shi kuma jigon littafin So Nakasar Rayuwa shi ne ‘Tarbiyya’, na nuna illar rashin tarbiyya da shigar da ba ta dace ba da matasanmu ke yi, shigar banza ba ta jawo ma mutum komai sai zubewar mutunci,l ittafin ya bayyana yadda mace za ta kasance mai kamewa da rikon addininta da shiga ta mutunci da kamala da yadda mata za su rinka sana’o’i a cikin gidajensu ta yadda za su dogara da kan su.

 

 

Wanne kalubale marubuta ke fuskanta a harkar rubutu?

Kalubalen da Marubuta ke fuskanta a harkar rubutu a yanzu za su kai biyu zuwa uku.

  1. Klubale na farko matsalar kasuwa ce, manya da kananan Marubuta na fuskabtar wannan matsalar, Marubuci zai fitar da kudi ya yi littafi amma ko rabin kudin ba su cika dawo ma sa ba, sai kadan-kadan.
  2. Kalubale na biyu kuma su ne marubutan kafar sada zumunta, Marubuta ne da rubutunsu ya tsaya iya kafar sada zumunta, sun taimaka sosai wajen durkusar da rubutu da Marubuta, ta hanyoyi da dama. Misali idan yau Marubuci/ Marubuciya ta fitar da littafi komai tsadarsa A ranar wadannan marubutan kafar sada zumunta din za su rubuce shi tas a kafar sada zumunta ana karantawa kyauta, ba tare da sun yi la’akari da kudin da marubutan suka kashe wajan fitar da littafin ba. Tsakani ga Allah suna cutar Marubuta sosai. Ga abu na yawo a kafar sadarwa kamar takardar tsire, dole kasuwar littafin ta mutu.
  3. Wani abin takaice shi ne, yadda wasu daga cikin marubutan kafar sada zumunta ke rubuta batsa karara a rubutunsu, ko ba sa tunawa akwai yaranmu kanana da suke amfani da kafar sada zumunta ta zamani? Wasu abin da suke rubutawa tamkar fim din batsa ne.

Wannan zai gurbata rayuwar ‘Ya’yanmu da jefa su cikin mummunar rayuwa, sannan ga tulin zunubi da za su daukar ma kansu. Ina kira ga marubutan kafar sada zmnta da su ji tsoron Allah su daina yada alfasha suna ma Marubuta zagi, idan za su yi rubutunsu, su yi mai ma’ana. Mi zai hana tunda suna da sha’awar rubutun su shigo cikin Marubuta su ma su zama marubutan na sosai.

 

Yaya kike ganin za a bullo wa matsalar nan?

Yadda za a bullo ma matsalar hanya ce mai sauki. Manyan Marubuta da kungiyoyin Marubuta su nemi wadannan marubtan kafar sada zmnta ko shuwagabanninsu, su zauna da su su nuna ma su abin da suke yi daidai da wanda ba su yi daidai, sannan su kwadaita masu amfaninsu idan suka zama Marubuta na sosai. Kamar misalin taron Marubuta Hausa na Duniya da za a yi, da zai yiyu sai a gayyato koda kadan daga cikinsu, tunda suna da kungiyoyi, idan a kai haka insha Allah za a samu fahimtar juna..

 

Ku na bukatar hukuma ta shigo cikin matsalar nan?

Sosai muna bukatar hukuma ta shigo sai dai mun sha kai kukanmu har yanzu ba a kai ga samun nasara ba.

 

 Wacce shawara za ki ba wa ‘yan uwanki marubuta?

Shawarata ga Marubuta daya ce, mu ci gaba da hada kanmu, sannan mu za mu ma su bincike a kan abin da muke rubutawa.

Exit mobile version