Kungiyar marubuta a kafafen sada zumunta ta ‘Arewa Media Writers’ ta bukaci al’ummar Najeriya, su kasance masu yada zaman lafiya, da kaunar juna da zamantakewa, a rubuce rubucen da suke yi a kafofin sada zumunta, na zamani. Shugaban kungiyar reshen Jihar Filato, Malam Abba Abubakar Yakubu ne, ya bayyana wannan bukata, a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida, bayan kammala babban taron shekara, da kungiyar ta gudanar a garin Jos, a karshen makon da ya gabata.
Har ila yau, ya shawarci marubuta su rika amfani da kafofin sada zumunta, wajen fahimtar da al’umma kan mahimman abubuwan da suke faruwa, tare da zaburar da shugabanni kan aikata mahimman abubuwan da suka kamata, ba zagi ko cin mutunci ba.
Malam Abba ya yi bayanin cewa an kafa wannan kungiya ce, da manufar hada kan marubutan Arewa karkashin inuwa daya, don yin magana da murya guda, ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta na zamani. Don a samar wa Arewa ci gaba, da mafita daga kalubale da take fuskanta.
Su ma da suke nasu bayanan, wasu daga cikin ‘yayan kungiyar, Abdulhadi Abdullahi Cokali da Mu’awuya Mai Dankali Jos da Hajara Muhammad, sun jaddada muhimmancin amfani da kafafen sada zumunta, wajen kawo sauyi mai amfani a cikin al’umma. Don haka, sun bukaci marubutan Arewa su hada kai, wajen samar wa Arewa mafita kan matsalolin da take fuskanta, ta hanyar amfani da kafafen sadarwar zamani.