Khalid Idris Doya" />

Maryam Yalwaji Katagum: ‘Yar Nijeriya Da Ta Yi Rawar Gani A Hukumar UNESCO

Misis Mariam Yalwaji Katagum, babbar jakadar Nijeriya a Hukumar kyautata ilimi da kimiya da al’adu ta majalisar dinkin duniya (UNESCO) tun daga watan Yunin 2009. A ranar 23 ga watan Yuli na 2019 ne shugaban kasa Muhammad Buhari ya zabe ta a matsayin daya daga cikin wadanda yake son nadawa Ministocinsa wacce ya zabo ta daga jihar Bauchi. Ta kasance tauraruwar Nijeriya a UNESCO wacce ta zagaya wurare daban-daban a fadin duniyar nan musamman a kan harkar ilimi.

Wace Ce Mariam Yalwaji Katagum?

Ta zo duniya ne a ranar 18 ga watan Nuwamban alif da 1954 a garin Azare da ke karamar hukumar Bauchi.

Bayan halartar karamin makaranta na farko da sakandare, ta garzaya zuwa jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ta samu shaidar digiri na farko a fannin harshen turanci (Ingilishi) a shekarar 1976, ta halarci digirinta na biyu (Masters) ne a jami’ar Legas inda ta karanci fannin gudanarwa da tsare-tsare a shekarar 1985, har-wa-yau a shekarar 1999 ne ta samu shaidar karatu a fannin tsare-tsaren bunkasa al’umma a kwalejin ilimi da ke Landan.

Ta fara aikinta ne a matsayin ‘yar bautar kasa (NYSC) wacce a hukumar albarkatun ruwa da ke garin Jos ta jihar Filato a shekarar 1977. Ta zama babbar jami’ar ilimi a kwalejin FGC da ke Azare a tsakanin 1981 zuwa 1984, ta kuma yi aiki a ma’aikatar samar da tallafin karatu ga dalibai ta gwamnatin tarayya a jihar Legas. A shekarar 1999 ta samu lambar shaidar girmamawa ta UNESCO.

An turata aiki a hukumar kula da ‘yan Nijeriya a UNESCO tsakanin 1985 zuwa 2000, ta taka matakai da mukamai wacce har ta zama sakatariyar sashi a UNESCO mai kula da zamantakewar al’umma da kimiyyarsu daga shekarar 2000 zuwa 2001, sannan an kuma nadata  Darakta kula da aiyuka na musamman a hukumar kula da makarantun firamare ta kasa da ke Abuja (NPEC) a shekarar 2001.

Ta zama Sakatare Janar ta Nijeriya a UNESCO kana aka kara kuma daura mata alhakin kula da bangarorin hadaka kan harkar ilimi ta kasa da kasa da ke ma’aikatar ilimi. A wannan lokacin ta yi aiki kafada-kafada da ma’aikatu daban-daban kamar su UNICEF, hukumar hadin gwiwa da kasashen duniya ta kasar Japan, wato Japan International Cooperation Agency (JICA), babban bankin duniya, sashin bunkasa kasa da kasa ta kasar Ingila (DFID), (COL) gami kuma da wasu kungiyoyin masu zaman kansu.

Maryam Yalwaji Katagum ta zama babbar Jakadiya ta Nijeriya a hukumar kyautata ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UMESCO), an nada wannan mukamin ne a ranar 1 ga watan Yunin 2009, ta kuma kama aiki ne a ranar 26 na watan Agustan 2009.

Kwamitocin da ta bayar da gudunmawa:

Maryam Yalwaji Katagum ta kasance mamba a kungiyoyi da daman gaske a bangaren aikinta, kadan da ga ciki sun hada da mamba a kwamitin amintattu na African Work Heritage Fund a tsakanin 2009 zuwa 2011; ta kasance shugabar kungiyar Mata a UNESCO daga 2009 zuwa 2012;  shugaba a kungiyar E-9 ta UNESCO daga 2010 zuwa 2012; mambar da ke wakiltar Nijeriya a Shalkwatan UNESCO daga 2011-2013.Wakazalika ta taba zama mamba da ke wakiltar ma’aikatar ilimi ta tarayya a majalisar zastarwa na kwalejin kimiyya da ke Kaduna, da ta jami’ar kimiyya na gwamnatin tarayya da ke Minna, jami’ar Legas.

Ta halarci tarukan kara wa juna sani da daman gaske gami da halarta taruka na kasa da kasa kan harkar ilimi a fadin kasashen duniya.  Kawo yanzu dai an tantance Madam, tana zaman jiran nadin shugaban kasa a hukumance ta zama daga cikin Minsitocin shugaban kasa Muhammad Buhari biyo bayan zabinta da shugaban ya yi a cikin Mukarraban da zai tafi da su a zangonsa na biyu, da ake wa lakabin ‘zangon Nes-Labul’.

Exit mobile version