Cibiyar Nazari da Binciken Tsaro ta Jamhuriyar Nijar ta gudanar da wani taro domin samo hanyar yaki da masu anfani da hanyoyin sadarwan zamani don kawo wa tsaro cikas.
Cibiyar ta ce, ta shirya taron ne domin musanan ra’ayi tare da sanin hanyoyin da za su bullo wa masu anfani da wannan hanyar domin cuta, danfara da yaudaran jama’ar kasa.
Mataimakin shugaban hukumar, AbdulAzeez Garba ya bada misali da kungiyar Boko Haram da ke anfani da hanyar sadarwan zamani wajen barbaza akidojin su.
Ya ce, taron zai nemo hanyoyin da za’a dakile irin wannan matsalar tare da cusa halin da’a ga masu anfani da hanyoyin sadarwan ta zamani.