Masana harkokin kudade da na tattalin arziki sun bukaci gwamnati da ta samar da manufofi tare da aiwatar da su da za su dakile matsalolin tattalin arziki wanda cutar Korona ta haddasa a cikin kasar nan, sannan sa bullo da hanyoyin zuba jari a cikin kasar nan. A cewarsa, daukan wadannan matakai zai bai wa Nijeriya damar fita daga cikin matsin tattalin arziki da kuma inganta samarwar abubuwan da ‘yan kasa suke bukata.
Masanan sun bayyana hakan ne a wajen wani taron harkokin kasuwanci da na kamfanoni wanda ya gudana a faifan bidiyo. Taron mai taken ‘mahimman abubuwan da Nijeriya ake tsammanin ta yi a bangaren tattalin arziki a shekarar 2021’, wannan ya yi dai-dai da dokar kudade da kuma dokokin harkokin kasuwanci na yankunan Afira.
Masanin harkokin tsare-tsare kudade kuma shugaban kungiyar haraji a Yammacin Afirka, Taiwo Oyedele ya bayyana cewa, duk da hauhawar farashi wanda ya kai na kashi 14.89 a shekarar 2020 da rashin ayyukan yi wanda ya kai na kashi 27 da cutar Korona da dokar hana zirga-zirga wanda ta shafi tattalin arziki da matsin tattalin arziki da talauci da dai sauran matsaloli, Nijeriya za ta iya samun dala biliyan 443 a fannonin tattalin arziki kafin kasarshen wannan shekarar, kamar yadda taron hukumar bayar da lamuni ta duniya karo na 26 ta bayyana. Oyedele ya kara da cewa, tabbas Nijeriya za ta fita daga cikin matsin tattalin arziki a shekarar 2021, amma wannan ya danganta ne da irin kokarin gwamnati da kuma bangaron masu zaman kansu.
Da ya ke gabatar da jawabi a wajen taron, ya bukaci kasar nan ta mayar da hankali a kan alfanun da ke cikin gudanar da gasa a cikin kasuwanci domin samun karfin tattalin arziki. Ya ce, an gudanar da wannan taro ne domin Nijeriya sa yi kokarin samar da manufofi da zai inganta harkokin kasuwanci.
Shugaban hukumar kula da ayyukan haraji , Olufunsho Ola-Ojo ya bayar da shawara a kan a dauki matakai masu tsauri a kan harkokin kasuwanci musamman ma a dai-dai lokacin da kasar nan take kokarin farfadowa daga matsin tattalin arziki.
A nasa bangaren, shugaban bankin Union Bank Nigeria Plc, Emeka Emuwa ya bayyana shekarar 2020 a matsayin shekarar da ya kamata a dauki mahumman darasi wajen samun hadin kai. Emuwa ya bayyana cewa, harkokin kasuwanci sun tabarbare wanda akwai bukatar samun hadin kai domin samun ci gaba mai daurewa.
Shararren masanin tattalin arziki, Cheta Nwanze ya bayyana cewa, tarihi ya nuna cewa ko shakka babau a Nijeriya ana samun rashin amana a cikin yarjejeniyar harkokin kasuwanci. Ya kara da cewa, akwai matsanancin talauci a cikin yankunan kasashen Afirka wanda yankunan suka kwashe shekara da shekaru suna fama da wannan matsala.
Ya ce, “akwai bukatar mu zuba jari na hadin gwiwa a tsakanin mutanen yankuna domin fita daga cikin matsalolin da muke fuskanta a halin yanzu. Haka kuma muna bukatar gwamnati ta samar da bayanan zuba jari a cikin kasar nan,” in ji shi.
A nasa jawabin, shugaban yanki na tattalin arziki kuma jakadar Faransa, Pascal Furth ya bayyana cewa, akwai mahimman takakai da dama da ke tsammanin Nijeriya za ta dauka wajen farfado da tattalin arzikinta, a dai-dai lokacin da Nijeriya ta fada cikin matsin tattalin arziki wanda ba taba ganin irin saba tun a shekaru 40 da suka gabata. Furth ya kara da cewa, a shirye kamfanonin Faransa da ke Nijeriya su taimaka wa kasar wajen farfado da tattalin arziki. Ya ce, kasar Faransa a tana neman hanyar da za ta bi wajen samarwa kasar Nijeriya kudade masu yawa a karkashin yarjejeniyar harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen guda biyu a shekarar 2021.