Rabiu Ali Indabawa" />

Masana Sun Bayyana Illolin Da ke Tattare Da Rage Darajar Naira

Masana sun bayar da illolin da ke tattare da rage darajar Naira ga tattalin arziki, wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi a kwanan nan a matsayinsa na hukumar da ke kulawa da sha’anin kudi.

A ranar 10 ga Yuli ne bayan kwanaki uku da rage darajar Naira, sai Dala ta tashi daga Naira 360 zuwa Naira 380.5 a kan Dala daya a kan farashin CBN.
Wani masanin kasuwancin ta na’urar lantarki mai suna Barrista Sani Kanabe da ke Jihar Legas, ya bayyana cewa, kafin rage darajar Naira a cikin harkokin kasuwanci sakamakon cutar Korona wacce ta haddasa saka dokar hana zirga-zirga a wasu bangarorin kasar nan, ana sayar da na’urar fotokwafi kan Naira 35,000. Amma sakamakon rage darajar Naira ya sa an samu karin a kan farashin kayayyaki musamman ma kayayyakin da ake shigowa da su kamar irin su motoci da kwamfutoci da kayayyakin daki da magunguna da sauran kayayyakin lafiya.
Wasu masana harkokin kasuwanci sun bayyana wa manema labarai irin illolin da ya ke tattare da rage darajar Naira. Sun bayyana cewa, rage darajar Naira ba karamin raunata tattalin arzikin kasa zai yi ba. Sun ce, ana samun kudaden shiga kashi 90 daga mai fetur wanda ake sayarwa a kasuwan duniya, sannan gwamnati tana gudanar da wannan kasuwanci ne da dala. Domin haka, za a samu matsala lokacin gwamnati ta ke bukatar Naira wajen gudanar da harkokin kasuwanci. Duk da kiran da masana su ke ta yi a kan gwamnati tarayyar Nijeriya ta mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arziki ta bangaren noma da ma’adanai da harkokin sadarwa da sauran fannoni na tattalin arziki, amma har yanzu gwamnati ba ta hankalta ba.
Haka kuma masana sun bayyana cewa, rage darajar Naira zai kara farashin kayayyakin da ake shigowa da su daga waje, sannan zai sa kamfanoni da yawa su durkushe domin ba za su iya sayan kayayyakin aiki ba.
Wani farfesa a bangaren kudade da kasuwanci mai suna Uche Uwaleke ya bayyana cewa, rage darajar Naira zai kawo cikas ga kasafin kudin shekarar 2020, domin an gabatar da kasafin kudin ne a kan duk Dala daya tana matsayin Naira 360, wanda a yanzu an samu kari a kan haka. Bayan haka kuma, za a samu karin farashi a kan mahimman kayayyaki sakamakon karin da za a samu na farashin mai.
“karin matsaloli dai ya hada da za a samu karin farashin mai da ake shigowa da shi musamman ma a yanzu da aka sake fasalin bangaren mai,” in ji Farfesa Uwaleke.
Wani shahararren masanin zuba jari mai suna Stephen Kanabe ya amince da bayanin da Uwaleke ya yi, ya bayyana cewa, akwai tsoron sayar da kadarori da karuwar basu ka sakamakon karancin da za a samu a bangaren zuba jari. Haka kuma zai shafi kasuwancin kasashen waje.
Shahararren masanin tattalin arziki mai suna Seye Adetunmbi ya bayyana cewa, matakin da CBN ta dauka ba zai haifar da da mai ido bag a kasar nan, sakamakon matsalolin da za a iya fuskanta na saye da sayarwa. Adetunmbi ya kara da cewa, mafi yawancin kamfanoni da masana’antu a Nijeriya za su mutu, kamar yadda bangaren wutar lantarki ta kawo matsaloli a cikin kasar nan.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa, yana da matukar mahimmanci a tabbatar da cewa an samu dai-daituwa a bangaren kasuwanci, ya kamata mahukunta a Nijeriya su tabbatar da illoli da ke tattare da duk wani manunofi da za su aiwatar. Sun shawarci hukumomin Nijeriya da su bunkasa wasu fannonin tattalin arziki kamar irin su noma da hakar ma’adanai da kuma karfafa kayayyakin cikin gida fiye da na waje.

Exit mobile version