CRI Hausa" />

Masana Sun Bukaci Hada Karfi Da Karfe Wajen Yaki Da COVID-19

Yayin da MDD ke bikin cika shekaru 75 da kafuwar dokar ayyukan ta a gobe Juma’a, masana a fannin ayyukan majalissar sun gudanar da wani dandali na tattaunawa ta kafar bidiyo a jiya Laraba 24 ga wata, inda suka jaddada bukatar dake akwai ga daukacin kasashen duniya, da su bunkasa cudanya da hadin gwiwa, wajen yakar cutar numfashi ta COVID-19, cutar da a yanzu haka ta zamewa duniya alakakai, take kuma ci gaba da yiwa harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar duniya kafar ungulu.

Ko da a baya bayan nan ma dai, sai da babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kashedin cewa, mai yiwuwa ne adadin masu dauke da cutar ta COVID-19 ya iya kaiwa mutum miliyan 10 a fadin duniya nan da makon dake tafe.
Jami’in ya ce ya zuwa yanzu, akwai sama da mutum miliyan 9.1 da ke fama da cutar, kuma sama da 470,000 sun mutu sanadiyyar harbuwa da ita a sassan duniya daban daban.
To amma a yayin da wannan hasashe na Mr. Tedros ke zama wata tunatarwa mara dadi, ga ta’azzarar yanayin da ake ciki game da yaduwar wannan cutar, ana iya cewa ra’ayinsa na bukatar daukar matakan gaggawa, da za mu iya takaitawa, da dakile yaduwar cutar, ya yi daidai da na wadancan masu ruwa da tsaki game da ayyukan MDD, wanda su ma ke ganin dacewar kawar da duk wani sabani da rashin jituwa, da siyasa, ta yadda dukkanin sassa za su ba da cikakkiyar gudunmawa don yakar wannan annoba.
Ko shakka babu, dukkanin sassan dake fatan ganin karshen wannan annoba sun amince cewa, hanya mafi dacewa ta shawo kan wannan cutar ba ta wuce hadin gwiwa tsakanin dukkanin kasashen duniya ba. Inda masharhanta da yawa ke ganin saurin dakile bazuwar cutar, na da alaka ta kai tsaye da yadda sassan kasa da kasa suka yi hanzarin ba da gudummawar da ta dace, a fannin shawo kan kalubalen da ake fuskanta, musamman a bangaren fadada gwaji don gano masu dauke da cutar, da kandagarki, da ma jinyar masu dauke da ita. Baya ga batun karfafa hadin gwiwar samar da magani da rigakafin ta.
Sauran sassan ayyuka masu muhimmanci sun hada da ci gaba da baiwa kasashe, da yankuna masu rauni tallafin da ya dace, wanda zai taimaka musu cimma nasarar yaki da cutar.
Wannan muhimmiyar gaba da masanan kasashen Sin, da Jamus, da Rasha, da Birtaniya suka samu, don gudanar da dandalin cika shekaru 75 da sanya hannu kan dokar ayyukan MDD, tamkar wata dama ce ga daukacin kasashen duniya, ta su sake kusantar juna, da yin aiki tare, don cimma buri guda, na kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makomar bai daya ga dukkanin bil Adama, wadda kowanne mutum dake doron duniyar nan zai ci gajiyar ta.
To sai dai kuma, yayin da ake ta fadi tashin cimma wannan buri, wasu sassan duniya na kokarin shatile kafar wannan manufa, ta hanyar yayata ra’ayin bangaranci da nuna son kai. Matakin da ko alama, ba zai yi musu amfani, ballantana ya amfani ragowar sassan duniya ba.
Irin wadannan matakai na nuna bangaranci da son kai, da kebe kai, da baiwa kasuwanni kariya, sun ci gaba da kawo baraka ga ayyukan yaki da cutar COVID-19, suna kuma dakile nasara, da ingancin matakan da ake dauka na yaki da cutar, duk kuwa da cewa, wannan cuta annoba ce da ta shafi duniya baki daya, wadda ba ta kebanta ga wani yanki, ko wani rukuni ko kabilun duniya ba.
Don haka dai duba da mahangar kwararru, da masana a fannin ayyukan MDD, ana iya cewa, hadin gwiwar dukkanin sassan duniya, da yin aiki tare, da kaucewa aikatawa, da furta kalaman kyama, kiyayya ko nuna bangaranci, da kawar da siyasantar da al’amura, su ne kadai za su kai duniya ga tudun mun tsira, a wannan yaki da daukacin bil Adama ke yi da cutar numfashi ta COVID-19. (Saminu Alhassan)

Exit mobile version