Masana sun nuna damuwarsu a kan shirin gwamnatin tarayya na amso bashin naira tiriliyan 5.39, domin cike gibin kasafin kudin shekarar 2021.
A cewar dokar kasafin kudin shekarar 2021, wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kwanakin da suka gabata ya nuna cewa, gwamnatin tarayya za ta ginginar da kadarorinta na naira biliyan 205.15. Lokacin da ya rattaba hannu a kasafin kudin shekarar 2021, shugaban kasa ya bayyana shirin amso bashi domin cike gibin da ke samu a tsakanin kudaden harajin da gwamnati take tsammanin a cikin kasafin kudin na naira tiriliyan 13.59. Ana tsammanin gwamnati za ta yi wa majalisa bayanin amso bashi a cikin ‘yan kwanakin nan.
Da take gabatar da bayani akan kasafin kudin, ministar kudi da kasafin da tsare-tsaren kasa, Misis Zainab Ahmed ta bayyana cewa, za a amso bashin naira tiriliyan 2.34 a cikin gida, sannan za a amso bashin naira 2.34 daga hanyoyi na kasashen ketare. Yayin da gwamnatin tarayya tana shirin amsho sauran naira biliyan 709.69 daga kasuwancin kasa da kasa. Wannan na nufin gwamnatin tarayya za ta amso jimillar bashi na naira 5.39 daga kasashen ketare da kuna kasuwancin cikin gida. Bashin zai kasance na kashi 33.99 a cikin kasafin kudin na naira 13.59. Yawan kudaden haraji da ake tsammanin samu a kasafin kudin shekarar 2021, ya kai na naira tiriliyan 7.89 fiye da na kashi 35 a cikin kasafin kudin shekarar 2020 wanda yaka yi wa garanbawul na naira tiriliyan 5.84.
Da yake mayar da martini a kan gibin kasaafin kudin, shugaban kungiyar kamfanoni na Jihar Legas, Dakta Muda Yusuf ya bayyana cewa, ci gaba da samun gibin kasafin kudi sannan ana amso bashi ba karamin abin damuwa ba ne. Ya kara da cewa, akwai bukatar daukan mataki mai tsauri a kan lamarin.
“Wannan zai shafi manyan ayyukanmu wajen gudanar da su daga basuka.
“Yawan harajin gwamnati da gwamnati take tsammanin samu shi ne naira tiriliyan 7.89, yayin da bashin da za a amso ya kai na naira tiriliyan 5.93, tazarar bai wuce tiriliyan 3.12. Wannan ba karamin abin takaici ba ne,” in ji shi.
Shima tsohon shugaban cibiyar inshore na Nijeriya, Richard Borokini yabayyana cewa, bashi yana zama mai kyau ne idan aka kashi kudaden ta hanyar fannonin tattalin arziki.
Ya ce, “idan gwamnati ta amso bashin kudade sannan ta kashe su wajen samar da ababan ci gaba kasa, to zai kara karfafa tattalin arziki a cikin kasa.
“Idan aka kashe kudaden basuka a kan inganta sufuri da bunkasa matatun mai da sauran abubuwa makamantan wadannan, zai taima wajen gudanar da harkokin kasuwanci a Nijeriya, sannan zai kara kawo ci gaban kasa.
“Amma idan gwamnati ta amso basuka ta kasa kashe kudaden nan ta hanyar da suka dace kamar irin biyan albashin ma’aikata, to wannan bashin yana da matukar illa ga kasa.”
A nasa bangaren, masanin tattalin arziki da ke jami’ar Ibadan, Adeola Adenikinju ya bayyana cewa, kudaden gudanar da manyan ayyuka suna da matukar mahimmanci. Ya bayyana cewa, Nijeriya da sauran kasashen
duniya sun fuskanci matsaloli a lokacin cutar Korona.
“Mun sami gibi a kasafin kudin shikarar da ta gabata, sannan wannan karoma mun sami haka, wannan ba zai ceto tattalin arzikin kasar nan ba.
“Ida nana bukatar fatfado da tattalin arziki, ya kamata a nemo hanyoyin samun kudaden haraji, amma ba dogaro da ambo bashi ba,” in ji shi.