Daga Muhammad Maitela,
Bayo bayan sake farfado da kamfanin leda da gwamnatin jihar Borno ta yi a karkashin Gwamna Babagana Umara Zulum, hukumar bunkasa ayyukan noma ta kasa (NALDA), ta yi odar fatar buhun leda masu nauyin kg50 miliyan biyu daga masana’antar da ke jihar.
Shugaban hukumar NALDA, Prince Paul Ikonne shi ne ya sanar da hakan a sa’ilin da ya jagoranci tawagar daraktocin sa kai wa Gwamna Babagana Zulum ziyara a ofishin sa a birnin Maiduguri.
Haka zalika, Mista Ikonne ya tabbatar da cewa hukumar NALDA za ta ci gaba da hadin gwiwa dangane da kayan da wannan kamfanin da ke jihar Borno ke samarwa, don bunkasa tattalin arziki.
Har wala yau kuma, ya ce shugaban NALDA ya shaida wa Gwamna Zulum cewa sun kawo ziyarar bisa umurnin shugaban kasa Buhari wajen sake farfado da gonakin da NALDA ta mallaka a sassan kasar nan daban-daban.
A hannu guda kuma, Mista Ikonne ya bayyana cewa an zabi jihar Borno tare da wata jihar daya a kasar nan, wanda a jihar Borno kadai za a horas da matasa 2,040 kiwon kifi.
A nashi jawabin, Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa tunanin farfado da kamfanonin jihar kokarin wanda ya gabace shi ne, Sanata Kashim Shettima a kyakkyawan fatansa na dora jihar Borno bisa ingantacciyar turbar raya fannin tattalin arziki.
“Saboda haka, dukan wadannan tsare-tsare domin habaka ayyukan noma da ka bayyana, a hakikanin gaskiya aikin wanda na gada ne, Hon. Kashim
Shettima bisa kyawawan manufofin sa wajen bunkasa aikin noma ta hanyar siyo wadannan na’urorin daga kasashe irinsu China, Turkiyya, India, Pakistan da Amurka.”
Zulum ya shaidar da cewa, duk da har yanzu wasu na’urorin basu fara aiki ba saboda matsalar tsaron da ta addabi jihar, wanda hakan ya dakatar da ayyukan noma a yankunan karkara.
A karshe Zulum ya bukaci NALDA ta bayar da muhimmanci wajen tallafa wa yan gudun hijira a sa’ilin da za ta aiwatar da wannan kuduri nata, na horas da manoma matasa, tare da taimaka musu da kayan, tare da bayyana cewa gwamnatin jihar Borno za ta yi aiki kafada da kafada da NALDA wajen ganin samun nasara.