Masana’antun Bauchi Za Su Ci Gajiyar Naira Biliyan Daya Daga Bankin Masana’antu

Kanana da matsakaitun masana’antu da suke Bauchi za su ci gajiyar rancen naira biliyan biya daga bankin masana’antu domin kyautata harkokin kasuwancinsu.

Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Bauchi, Alhaji Muhammad Sadik shine ya sanar da hakan a lokacin bude kasuwar baje kolin kayayyaki ta kasa na farko a jihar Bauchi mai taken (sabon hanyar farfado da tattalin arzikin kasa ta hanyar mai da hankali kan gudumawar da kanana da matsakaitun sana’o’i) da aka gudanar a filin taro na tunawa da Ibrahim Babadamasi Babangida Skuare Bauchi.

Sadik ya ce, an samu kaiwa ga cimma wannan nasarar ne biyo bayan ziyarar da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya kai kwanakin baya ga Manajan Gudanarwa na masana’antu a Abuja.

Ya ce, gwamnatin jihar za ta taimaki kananan ‘yan kasuwarta domin su samu cin gajiyar rancen kudaden daga bankin masana’antu a kokarinsu na farfado da masana’antu a jihar domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Kwamishinan ya bayyana cewar ma’aikatar kasuwanci da masana’antu za su ci gaba da tabbatar da yin aiyukan da suka dace domin su yi daidai da tsare-tsare da manufofin gwamnatin jihar na bunkasa tattalin arzikinta.

 

A cewar shi; wannnan ci gaban zai taimaka sosai wa ‘yan kasuwar domin su habaka sana’arsu domin su ma su gwanance, tabbatar da samar da masana’antu masu zaman kasuwa da ci gabantar da su, inganta hanyoyin zuba jari da kuma kyawawan tsari da za su taimaka wurin samar da aiyukan yi.

Kwamishinan ya kuma ce, kasuwar baje kolin zai yi gayar kyautata hada-hadan kasuwanci a shiyyar arewa maso gabas da ma kasa baki daya, yana mai bayar da tabbacin gwamnatin jihar da ke ci a yanzu na tabbatar da janyo kasuwar baje kolin akai-akai domin amfana da dumbin fa’idar da hakan ke da shi.

Ya kuma ce, jama’a daga sassa daban-daban da ‘yan kasuwa sun halarci wannan bajen kolin da yanzu haka haka yake ci gaba da gudana a jihar, yana mai nuna gamsuwarsa da yadda masu ruwa da tsaki kan harkar kasuwanci da baje kolin suka amshi gayyatarsu hannu biyu-biyu kana suka zo domin baje hajarsu.

Kwamishinan ya kuma yaba da kokarin wadanda suka zatse damtse wajen tabbatar da kasuwar ta kai ga haduwa har ta kai ga kankama, ya nuna rawar da gwamnan jihar Bala Muhammad ya taka a matsayin rawa mai kyau da yayi domin kawo wa jama’ansa ci gaba mai ma’ana.

Daga bisani ya kuma gode wa hukumomi da kungiyoyi daban-daban da suka bayar da tasu gudunmawa, “Ina mika godiya ta musamman ga wadanda suka tabbatar da kasuwar baje koli ta farko a jihar Bauchi ta kai ga iyuwa irin su, Jami’an sojin kasa, Nigerian Maritime Authority & Safety Agency (NIMASA), Federal Inland Rebenue Serbices (FIRS), Institute of Agricultural Research, ABU Zaria, FARSMAN Ltd, Nigerian Edport Promotion Council, Nigerian Building & Road Research Institute (NBRRI), Bauchi Inbestment Corporation, Alind Wire & Cables Limited, Zaranda Hotel Limited, AYM Shafa Limited, Techno Shalangwa Nigeria Limited, Bauchi State Internal Rebenue Serbice da kuma kananan hukumomi 20 na jihar,” A cewar shi.

Karamar Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Ambasado Maryam Yalwaji Katagum ita ce ta bude kasuwar baje koli na farko da ake ci yanzu haka a Bauchi.

Exit mobile version