Garin Gyirong yana birnin Rikaze na jihar Tibet ta kasar Sin, Allah ya albarkaci wurin da dazuzzuka, yanayi mai kyau da kuma al’adun kalibar Zang iri daban daban. A kauyen Rema dake wannan gari, akwai wani kamfanin shuka nau’o’in laimar kwado, mai suna kamfanin kimiyya da fasahar halittu na Rema.
A shekarar 2015, an samu karin mutane dake zuwa yawon shakatawa garin Gyirong, hakan da ya sa, aka sayar da dukkanin maganin gargajiya na Lingzhi da kuma Tianma na wurin. Wannan ya sa, malam Ou Zhu ya tafi birnin Linzhi domin koyon fasahohin shuka maganin gargajiya na Lingzhi da Tianma da sauransu. Sa’an nan, ya yi nasarar shuka maganin gargajiyar, har ya sayar da su baki daya a bana. Lamarin da ya baiwa manoman wurin kwarin gwiwa, har mutanen kauyen da dama suka fara rungumar wannan sabon aiki.
A sa’i daya kuma, gwamnatin wurin ta taimakawa malam Ou Zhu don ya kafa kamfanin hadin gwiwa, ta yadda, zai taimakawa mazaunan wurin wajen samun karin kudin shiga. A bana, bisa goyon bayan da gwamnatin ta ba su, an sake habaka kamfanin hadin gwiwar, har ya taimaka matuka wajen samar da guraben aikin yi ga mazaunan wurin.
Kana, sabo da karuwar bukatun maganin gargajiya a kasuwanni, Ou Zhu ya ci gaba da habaka masana’antun shuka Lingzhi da Tianma a bana, da kara yawan nau’o’in kayayyakin da ya shuka. Har ya gayyaci masu fasahar shuka maganin gargajiya a kamfaninsa domin su horas da ma’aikatan kamfanin. A sa’i daya kuma, yana dukufa wajen hada harkokin kamfaninsa da sana’ar yawon shakatawa, domin samar da karin guraben aikin yi ga mazauna wurin. (Mai Fassawara: Maryam Yang)