Masani: Amurka Take Yada Karairayin Aikin Tilas Don Bata Sunan Kasar Sin
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masani: Amurka Take Yada Karairayin Aikin Tilas Don Bata Sunan Kasar Sin

byCMG Hausa
3 years ago
Amurka

Wani kwararren Ba-Amurke ya ce, “Ni a ra’ayi na, batun dokar aikin tilas ta Uyghur, ba komai ba ne illa makircin siyasa da aka kirkira domin bata sunan kasar Sin.

Daniel Kovalik, wani lauyan kasar Amurka dake koyar da hakkin dan Adam na kasa da kasa a kwalejin nazarin dokoki na jami’ar Pittsburgh, ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, “Hakika dai, wannan ba batu ne da ya shafi hakkin dan Adam ba, tabbas. Sai dai kawai, batu ne da ya shafi yunkurin gwamnatin kasar Amurka na neman shafawa kasar Sin bakin fenti da zubar mata da kima.”

  • Ma’aikatar Wajen Kasar Sin Ta Musanta Kalaman Amurka Da Birtaniya Game Da Yankin Hong Kong

Kasar Amurka tana amfani da batun hakkin dan Adam a matsayin wani salon makirci domin yakar dukkan wadanda take son lalata hulda da su a cewar Kovalik.

Ya ce, lamarin ba shi da wata alaka da batun hakkin dan Adam, kawai dai batu ne da ya shafi moriyar Amurka ta fannonin tattalin arziki da manyan tsare-tsare.

A cewar masanin, babu abin da ya shafe su da hakkin dan Adam na kasar Sin, abin da kawai ya dame su shi ne, kasar Sin ta zama wata babbar mai fada-a-ji ta fannin tattalin arziki a duniya, kuma mai karfi ta fuskar diflomasiyya.

Kana suna yunkurin fakewa da batun hakkin dan Adam ne wajen lahanta kasar Sin kasancewar suna daukar Sin a matsayin babbar abokiyar takarar tattalin arziki.

Kovalik ya kara da cewa, “Ina tsammanin abin da kawai ya fi dacewa shi ne kasar Sin ta ci gaba da abubuwan da take yi, ta kara matsawa gaba, ta ci gaba da ayyukan gina hanyoyin mota, da jiragen kasa, ta ci gaba da ayyukan samar da dawwamamman ci gaba, da tsame mutane daga kangin talauci.”
Ya ci gaba da cewa, kamata ya yi Sin ta ci gaba da abubuwan da ta sanya a gabanta.

Duniya tana kallon yadda kasar Sin take. Batun yada farfagandar kasashen yammacin duniya ba zai taba sanyaya gwiwar kasar Sin kan manufofinta ba.(Ahmad)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Hadin Lemon ‘Ya’yan Itatuwa

Hadin Lemon 'Ya'yan Itatuwa

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version