Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Masani: Kasar Sin Ba Za Ta Yi Wa Sauran Kasashe Zalunci Ba

by
1 year ago
in DAGA BIRNIN SIN
3 min read
Masani: Kasar Sin Ba Za Ta Yi Wa Sauran Kasashe Zalunci Ba
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Kasuwannin Shanghai Suna Dawowa Bakin Aiki Bisa Matakai Daban Daban Tun Daga Yau

Hukumar Kididdigar Sin: Za A Daidaita Tasirin Da COVID-19 Ke Haifarwa Tattalin Arzikin Kasar

Raul Sorrosa, shi ne wani shahararren masanin ilimin zaman al’umma, kana mai nazarin al’amuran siyasa, na kasar Ecuador. Ya gayawa wakilin babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG a kwanan baya cewa, kasar Sin ba za ta taba yi wa sauran kasashe zalunci ba, domin tana bin akidar hadin gwiwa tare da saura don tabbatar da moriyar kowa. Mista Raul Sorrosa ya ce, yana zumudin ganin fara taron shugabannin kasashen Sin da na gabas da tsakiyar nahiyar Turai. a cewarsa, a cikin shekarun da suka gabata, kasar Sin da kasashen gabas da tsakiyar Turai sun yi ta kokarin karfafa hadin gwiwarsu, inda manyan jami’an kasashen suka ziyarci juna a kai a kai, kana an yi kokarin gudanar da ayyuka masu alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”. Game da hadin gwiwar kasashen a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da aikin ilimi, da al’adu, an samu nagartaccen sakamako, tare da kyautata tsare-tsarensu na hadin kai da juna. Sorrosa na ganin cewa, wani sako mai kyau da taron na wannan karo zai nuna wa duniya, shi ne wani ra’ayi na kin dunkulewar kasashe daban daban, da kokarin kare kai, gami da ta da yake-yaken ciniki, wanda ya taba yaduwa a duniya a lokacin da Donald Trump ke mulkin kasar Amurka, zai kai karshensa. A nata bangare, kasar Sin za ta iya taimakawa mai da kasashen Turai a matsayin cibiyar jigilar kayayyakin da aka samar da su a kasashe daban daban, don magance samun shingayen da za su hana jigilar kayayyaki. Kana kasar Sin ta nanata ra’ayinta na kasancewar bangarori masu fada a ji da yawa a duniya, da alkawarin da ta dauka na girmama mulkin kai na sauran kasashe, da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidansu.
Yanzu haka, Mista Sorrosa yana zama a kasar Czekh, don haka shi ma ya yi tsokaci kan huldar dake tsakanin kasar Sin da kasar Czekh. A cewarsa, kasashen 2 za su kara kyautata huldar dake tsakaninsu a nan gaba. Sorrosa ya ce, kasar Sin ta riga ta zama wata babbar kasa mai karfin tattalin arziki, bayan da ta kwashe shekaru fiye da 40 tana kokarin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje. Don haka, ya kamata jama’ar Czekh su lura da muhimmancin kasar Sin. Da ma kasar Czekh na bukatar shigowa da dimbin kayayyaki daga sauran kasashe, kana ingantattun kayayyakin da ake samarwa a kasar na bukatar samun kasuwannin da za a rika sayar da su. Kana kasar Sin za ta iya biyan bukatun kasar Czekh daga dukkan fannonin guda 2. Misali, a shekarun baya bayan nan, an samu sayar da motocin samfurin Skoda kirar kasar Czekh da yawa zuwa kasar Sin. Ba domin kasuwannin kasar Sin ba, da tuni ma’aikata dubu 33 na kamfanin Skoda sun fuskanci matsalar rashin aikin yi. Kana yadda ake samun koma bayan tattalin arziki a kasar Czekh sakamakon annobar COVID-19 shi ma ya shaida muhimmacin masu yawon bude ido Sinawa ga sha’anin yawon shakatawa na kasar. A cewar Mista Sorrosa, kasar Sin aminiya ce, ba abokin gaba ba. Abun farin ciki shi ne, shugaban kasar Czekh Milos Zeman, da magabacinsa Vaclav Klaus, dukkansu suna son karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin. Ma iya cewa suna dora muhimmanci ne kan samun takamaiman ci gaba a kasarsu.
Ban da wannan kuma, Mista Sorrosa ya bayyana ra’ayinsa dangane da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka. Ya ce, kasar Sin ba ta taba yin mulkin mallaka a yankin Latin Amurka ba. Tushen huldar kasashen yankin Latin Amurka da kasar Sin shi ne kokarin haifarwa juna da moriya. Saboda haka, Mista Sorrosa ya shawarci kasashen Latin Amurka da su kara kokarin hadin kai tare da kasar ta Sin, don neman samun karin ci gaban kasa.
Raul Sorrosa ya kara da cewa, zuwa yanzu kasar Sin ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. Amma idan mun waiwayi yadda tattalin arzikin kasar yake wasu shekaru 50 da suka wuce, za a ga tattalin arzikin kasar bai kai na Mexico ko kuma Ecuador ba a lokacin. Ci gaban tattalin arziki da kasar Sin ta samu cikin wadannan shekaru 50, ya sa kasar ta zama wata babbar kasa dake taka rawar gani a al’amuran siyasa da tattalin arziki na kasa da kasa. Koda yake, har yanzu kasashen yammacin duniya na mai da dalar Amurka a matsayin ginshikin tsarin hada-hadar kudi ta duniya, amma za a iya kyautata zaton cewa kudin Sin RMB zai kara taka muhimmiyar rawa a duniya. (Bello Wang)

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Ciki Da Gaskiya Wuka Ba Ta Huda Shi

Next Post

Kasar Sin Ta Tura Kashin Farko Na Gudummawar Alluran Riga Kafin COVID-19 Zuwa Afirka

Labarai Masu Nasaba

Kasuwannin Shanghai Suna Dawowa Bakin Aiki Bisa Matakai Daban Daban Tun Daga Yau

Kasuwannin Shanghai Suna Dawowa Bakin Aiki Bisa Matakai Daban Daban Tun Daga Yau

by CMG Hausa
12 hours ago
0

...

Hukumar Kididdigar Sin: Za A Daidaita Tasirin Da COVID-19 Ke Haifarwa Tattalin Arzikin Kasar

Hukumar Kididdigar Sin: Za A Daidaita Tasirin Da COVID-19 Ke Haifarwa Tattalin Arzikin Kasar

by CMG Hausa
13 hours ago
0

...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Sanarwar G7 Kan Batun Kasar Sin Karya Ce Zalla

Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Sanarwar G7 Kan Batun Kasar Sin Karya Ce Zalla

by CMG Hausa
13 hours ago
0

...

Annobar COVID-19 Ba Za Ta Hana Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Yadda Ya Kamata Ba

Annobar COVID-19 Ba Za Ta Hana Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasar Sin Yadda Ya Kamata Ba

by CMG Hausa
13 hours ago
0

...

Next Post
Kasar Sin Ta Tura Kashin Farko Na Gudummawar Alluran Riga Kafin COVID-19 Zuwa Afirka

Kasar Sin Ta Tura Kashin Farko Na Gudummawar Alluran Riga Kafin COVID-19 Zuwa Afirka

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: