CRI Hausa" />

Masanin Amurka: Cewar COVID 19 Ta Samo Asali Daga Wuhan Kuskure Ne

Kwanan baya, farfesa Robert Garry na jamiar Tulane dake kasar Amurka, ya zanta da manema labarai na kafar ABC, inda ya bayyana cewa, kasuwar sayar da naman teku dake birnin Wuhan ba ita ce asalin cutar COVID-19 ba.

A cikin zantawar tasu, Garry ya cewa, ko da yake, mutane da dama na ganin cewa, kwayar cutar ta samo asali ne daga wata kasuwa dake birnin Wuhan, amma wannan raayi ne mai cike da kuskure. A cewarsa, binciken da yake yi, da sauran nazari da aka yi na nuna cewa, wannan cutar ta samo asali ne daga wani wuri daban, kuma ba shakka akwai mutanen da suka kamu da cutar a Wuhan, amma ba nan ne mafarin cutar ba.
Garry ya kuma kara da cewa, irin wannan kwayar cuta da ba ta kawo illa mai tsanani, ta yadu a tsakanin Bil Adama cikin gwamnan shekaru.
Ban da wannan kuma, Garry ya ce, daga bincike kan sauran irin wannan kwayar cuta an gano cewa, wannan kwayar cuta na iya sauya halayenta, daga bisani ta zama mai saurin yaduwa, wanda hakan ne dalilin saurin yaduwar COVID-19 a halin yanzu.


Dadin dadawa, rukunin masu bincike karkashin farfesa Garry, ya ba da sakamako cikin bayanin da ya wallafa a kan mujallar Nature Medicine cewa, kwayar cuta ta COVID-19 na bullo ne daga indallahi. (Mai Fassarawa: Amina Xu)

Exit mobile version