Masanin Amurka: Ya Dace A Gano Asalin Cutar COVID-19 Domin Kandagarkin Barkewar Annoba A Nan Gaba

Daga CRI Hausa

Babban makasudin gano hakikanin tushen cutar COVID-19 shi ne domin daukar matakan hana barkewar wasu annobar a nan gaba karkashin hadin gwiwar kasa da kasa, maimakon zarge zarge ko kuma neman bata sunan wasu kasashe, wani farfesa a jami’ar kasar Amurka ne ya bayyana hakan.

Batun tambaya game da asali ba batu ne da ya shafi wannan gwamnatin ko waccar ba, kana ba batu ne dake shafar wata shiyya ko kuma zargi kan kasar Sin da dora alhakin kan Amurka ba, Jeffrey D. Sachs, daraktan cibiyar samar da dawwamamman ci gaba ta jami’ar Columbia, kana shugaban shirin gamayyar samar da dawwamamman ci gaba na MDD shi ne ya wallafa wannan batu.

Kamata ya yi masanan kimiyya, da ‘yan siyasa, da kwararru, da masu fashin baki kan al’amurra a kafafen sada zumunta sun fahimci cewa illolin dake tattare da annobar tamkar samar da wata fitila ne da ya kamata a haska wajen dakile barkewar annoba a nan gaba, masanin ya bayyana hakan ne cikin wani sharhi da aka wallafa a ranar Alhamis wanda gidan talabijin na CGTN na kasar Sin ya watsa.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)

Exit mobile version