CRI Hausa" />

Masanin Najeriya: Akwai Makoma Mai Haske Ga Huldar Najeriya Da Sin

A ranar 12 ga watan Fabrairun shekarar 2021, daraktan cibiyar nazarin al’amurran kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju, ya wallafa wani sharhi mai taken, “Dabarun ci gaban Najeriya da kasar Sin nan da wasu shekaru 50 masu zuwa” a wata shahararriyar kafar yada labarai ta The National. Masanin ya tabbatar da cewa, an samu bunkasuwar hulda cikin sauri a tsakanin kasashen biyu tun bayan da Najeriya da Sin suka kulla huldar diflomasiyya shekaru 50 da suka gabata, kuma ya yi amanna cewa kafa ingantaccen salon kyautata alakar dake tsakanin kasashen biyu a shekarar 2005 ya kafa wani muhimmin tarihi game da hadin gwiwar bangarorin biyu. Muddin Najeriya ta yi kyakkyawan amfani da wannan damar wajen inganta alakar abokantakar dake tsakanin Najeriya da Sin, to akwai wasu karin muhimman sakamakon da za a cimma nan da wasu shekaru 50 masu zuwa.

Sharhin ya bayyana cewa, hadin gwiwar Najeriya da Sin a fannoni da dama, akwai yiwuwar samun manyan sakamako da ake hasashen a nan gaba. Kasar Najeriya tana da muhimman damammaki na albarkatun ‘yan kwadago da kuma saukin farashin kudaden gudanar da ayyuka wanda kasar Sin ke da shi a farkon lokacin kaddamar da manufarta ta yin gyare gyare a gida da bude kofa ga waje. Ya kamata Najeriya ta yi kyakkyawan amfani da damammakin sauye sauyen tsarin tattalin arziki irin na kasar Sin, da daga matsayin tsarin masana’antunta da karfafa dabarun hadin gwiwa wajen yin musayar tsarin ayyukan masana’antu. Yayin da kasar Sin ta kasance babbar kasuwa da kuma fatan da ake da shi ga tsarin yarjejeniyar cinikayya cikin ‘yanci ta nahiyar Afrika, ya kamata Najeriya ta yi kokarin inganta tsarin masana’antunta da karfinta na samar da kayayyaki tare da taimakon kasar Sin, domin zama kasa mafi samar da kayayyaki da fitar da su zuwa ketare, maimakon zama cibiyar sayan hajoji. A lokaci guda kuma, ya kamata Najeriya ta yi koyi da kasar Sin daga irin nasarorin da ta samu wajen yaki da fatara da tsarin shugabanci na gari, ta fadada yin musayarta da kuma karfafa hadin gwiwa a tsakanin kwararrun kasashen biyu, kana ta yi aiki tare da kasar Sin wajen cimma nasarar tsarin gamayyar bangarori daban daban da kyautata tsarin demokaradiyya bisa dokokin kasa da kasa.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)

Exit mobile version