Masanin Tattalin Arzikin Amurka: Akwai Bukatar Amurka Ta Yi Hadin Gwiwa Da Sin Don Yakar COVID-19

Daga CRI Hausa,

Sanannan masanin tattalin arzikin nan na Amurka, Jeffrey Sachs, ya ce tilas ne Amurka ta yi aiki tare da kasar Sin domin samarwa duniya mafita don kawo karshen yaduwar annobar COVID-19, masanin wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da kafar yada labaran kasar Malaysia wanda aka wallafa a yau Lahadi.

A yayin tattaunawarsa ta hanyar email da jaridar Star ta kasar Malaysia, Sachs ya ce, matakan yaki da annobar a duniya sun yi matukar karanci, kuma daya daga cikin manyan matsalolin dake haifar da koma baya a yaki da annobar a shiyyoyin duniya shi ne rashin hadin kai tsakanin kasashen Amurka da Sin don yin aiki tare wajen nemawa duniya mafita.

“Wannan abin takaici ne, tun da kasar Sin ta yi aiki mai kyau wajen nasarar dakile annobar, to ya kamata duniya ta koyi darrusa masu yawa daga irin matakan da kasar Sin ta dauka,” in ji masanin tattalin arzikin na Amurka, wanda ke jagorantar hukumar yaki da annoba ta Lancet, wacce aka kirkira da nufin taimaka wajen gaggauta yaki da annobar a duniya, da samar da daidaito, da kuma hanya mafi dacewa a yaki da annobar.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)

Exit mobile version