A ranar Asabar kasar Masar ta sanar da cewa ta bayar da lasisin amfani da allurar riga-kafin annobar COVID-19 wadda kamfanin hada magunguna na kasar Sin Sinopharm ya samar a hukumance domin amfanin gaggawa a kasar.
A wani shirin talabijin da aka gudanar a kasar ranar Asabar, ministar lafiyar kasar Masar Hala Zayed ta ce hukumar kula da magunguna ta kasar Masar EDA, ta bayar da lasisin yin amfani da riga-kafin wanda kasar Sin ta samar don bukatun gaggawa.
Masar ta amshi kason farko na allurar riga-kafin kamfanin Sinopharm a ranar 10 ga watan Disambar shekarar 2020. Ministar ta ce kashin farko na riga-kafin ya shiga zagaye na hudu na gwaje-gwajen da hukumar EDA ta gudanar kuma dukkan gwaje-gwajen sun tabbatar da ingancin riga-kafin. Ta kara da cewa, Masar tana sa ran karbar kashi na biyu na riga-kafin cutar ta COVID-19 a nan wasu kwanaki masu zuwa, wanda ake sa ran yiwa ‘yan kasar a cikin watan Janairu.
Tun farkon barkewar annobar COVID-19, kasashen Masar da Sin suke cigaba da yin hadin gwiwa domin yakar annobar ta hanyar musayar tallafin kayayyakin kiwon lafiya da na kwararru. (Mai Fassarawa: Ahmad Inuwa Fagam)