Daga Khalid Idris Doya,
Masarautar Bauchi ta amince da dakatarwar gaggawa ga sarautar gargajiya na ‘Jakadan Bauchi’ da aka nada wa tsohon Kakakin Majalisar Dokokin ta tarayya, Hon. Yakubu Dogara.
Galadiman Bauchi, Surveyor Ibrahim Sa’idu Jahun shi ne ya sanar da dakatarwar a ganawarsa da ‘yan jarida a ranar Litinin.
Ya yi bayanin cewa, daukan wannan matakin ya biyo bayan zargin da aka yi na hannun Dogaran a rikicin baya-bayan nan da ya auku a karamar hukumar Bogoro lokacin bikin tunawa dan gwagwarmaya nema wa al’ummar Sayawa ‘yanci, marigayi Baba Peter Gonto wanda har hakan ya jawo kai wa sarakunan Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu da na Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Othman hari tare da farfasa musu motoci.
Masarautar ta nuna damuwarta ainun dangane da batun da ta samu na cewa akwai hannun jigo kuma daya daga cikin masu rike da Sarautar gargajiya wajen tunzura matasa kai hare-haren ga wadanda ba su ji na su gani ba.
Masarautar ta nuna bacin ranta da mamaki dangane da cewa shi Yakubu Dogara wanda ke rike da Sarautar Jakadan Bauchi bai jajanta wa sarakunan da lamarin ya shafa ba, balle ya nuna ba hannunsa cikin lamarin rikicin da ya faru a yayin tunawa da Baba Gonto a ranar 31 ga watan Disamban 2021 a Karamar Bogoro da Tafawa Balewa.
Kan hakan ne ya karanto matsayar masarautar, “Don haka, Masarautar Bauchi ta dauki matsayar dakatar da Sarautar Jakadan Bauchi nan take har zuwa lokacin da kotu za ta kammala sauraron karar da aka shigar kan wannan lamarin.”
Idan za ku iya tunawa dai, Gwamnatin jihar Bauchi a karkashin Sanata Bala Muhammad ta maka tsohon Kakakin tare da wasu a kotu bisa zarginsu da hannu a rikicin da ya jawo kashe-kashe, kona motoci, kadarori da tada zaune tsaye wanda aka zargi wasu fusatattun matasa da yi.
Sannan rikicin ya jawo banka a wajen taron wuta, gidajen mutune, motoci da kadarori, tare da kai hari wa Sarkin Bauchi da Dass.
Masarautar a wani zaman gaggawa da suka yi a ranar 4 ga watan Janairun 2022 sun yi tir da harin tare da kira ga Gwamnatin jihar da ta tarayya da su kafa kwamotovin bincike domin gano masu hannu a lamarin domin hukuntasu.