Muazu Hardawa" />

Masarautar Bauchi Ta Nemi A Tallafa Wa Wadanda Ta’adin Iska Da Ruwa Ya Shafa

Mai martabar Sarkin Bauchi Alhaji Dokta Rilwanu Sulaimanu Adamu ya nuna damuwa tare da wanke masarautar daga zargin da ake yi mata na rike kudin agajin da ake bayarwa domin taimakon wadanda annobar iska da ruwa ta musu barna a ciki da wajen garin Bauchi kusan makonni uku da suka gabata.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kwamitin da gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya kafa domin duba barnar tare da tantance mutanen da suka samu kan su cikin wannan ibtila’i wanda ya auku kusan kwanaki 20 da suka gabata. Inda Sarkin ya bayyana cewa ya samu koke koke da korafi mai yawa daga mutane game da yadda ake raba kayan da ake bayarwa don tallafawa mutanen da wannan masifa ta shafa inda wasu mutane ke ganin kamar an ba masarautar kudi ko kayayyaki amma ta rike bata bayar ba. Ya ce maganganun da ke fitowa daga bakin mutane babu dadi saboda yadda lamurra ke gudana ya zamo wajibi yayi bayani don kowa ya san halin da ake ciki. Don haka ya bayyana cewa tun daga faruwar wannan matsala an kafa kwamiiti kuma duk abin da aka kawo fadarsa suna turawa kwamitin don ganin an yi abin da ya dace.
Don haka ya bayyana cewa taimakon da aka samu a fadar sa shi ne wanda tsohon mataimakin shugaban kasar Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayar na Naira Milyan goma kuma tuni ya mika cakin kudin wa kwamitin da aka kafa din yin abin da ya dace. Ya kara da cewa gwamna Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe shima ya bayar da naira milyan goma, akwai kuma motocin Maya da na abinci duk an hannata ga kwamitin sun raba wasu kayan wasu kuma ana kan rabawa.
Sai kuma shugaban kantin jifatu shima ya bayar da tallafin buhunna dari na abinci duk an mika wa Yan kwamitin.
Bayan haka kuma shugaban kamfanin mai na kasa NNPC Dokta Mai Kanti Baru shima ya zo ya yi jaje kuma ya ce za su aiko da cakin kudi na naira milyan 50 don a rabawa mutanen amma har yanzu ba a aiko da kudin ba suna tsammanin isowar cakin da ya ayyana cewa zai aiko idan ya USO zai mikawa kwamitin.
Don haka ya ce daga wannan babu wani abun da aka kawo masarautar Bauchi don rabawa mutanen da wannan matsala ta shafa daga masu zuwa jaje.
Dokta Rilwanu Sulaimanu Adamu ya kara da cewa yaji korafi mai yawa game da yadda aka raba kayan abinci da aka bayar wa masu unguwanni, inda aka rika samun sama da fadi daga masu unguwanni da ‘yan siyasa ake kukan rijiya ta bayar da ruwa guga ya hana, don haka ya ce duk wani mai korafi kan haka ya sanar da shi kuma a shirye yake wajen ganin ya hukunta duk wani mai unguwa da aka samu da laifin danne kayan wadanda matsalar ta shafa saboda abu ne da bai dace ba saboda rashin tausayi mutanen da suka shiga mawuyacin hali madadin a taimaka musu amma a rike abin da aka bayar domin tallafa musu idan had an bayar kenan.
Don haka Sarkin Bauchi ya bayyana damuwa game da karancin kayan tallafin ga mutanen da wannan matsala ta shafa.
Kusan makonni uku kenan da aukuwar annobar da ta shafi gidaje da filaye a kalla dubu goma, wacce ba a taba ganin irinta ba a garin Bauchi da kewaye. Kuma kusan mutane dari suka rasa rayukan su yayin da mutane da dama suka samu munanan raunuka bar zuwa wannan lokaci babu wani tallafin azo a gani daga gwamnati jiha ko ta tarayya illa kayan abinci da suka kunshi shinkafa da masara da garin rogo da tabarmai. Yawancin rabon kuma ana korafin an raba daga mudu daya zuwa mudu biyar ne kowa ya samu. Wasu kuma har zuwa wannan lokaci ko sannu ba wanda take inda suke daga gwamnati ya musu.
Duk da cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya zo jihar Bauchi don jajentawa amma har Yau babu wani tallafin gwamnatin jiha ko tarayya da aka bayyana. Yayin da wadanda ke asibiti da Wanda suka warke suma babu wani taimakon gwamnati da su ka samu har zuwa wannan lokacin in baicin na mudun masarar da a kullum a ke korafi kansa.

Exit mobile version