Masarautar Dutse Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Algus

Majalisar masarautar Dutse ta bayyana cewa a shirye ta ke da ta yi aiki tare da duk wata hukuma da ta kuduri aniyar inganta rayuwar al’umma.

Mai Martaba Sarkin Dutse, Dakta Nuhu Muhammad Sunusi, ne ya bayyana haka lokacin da babban jami’in hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa da ke jihar Jigawa, Muhammad Alhaji Bukar, ya kai ma sa ziyarar ban-girma a fadarsa.

Mai Martaba Sarki ta hannun Babban Dan Majalisar Sarki kuma Galidiman Dutse, Alhaji Basir Muhammad Sunusi, ya wakilta, ya ce akwai gagarumin aiki a gaban hukumar don kuwa sai sun wayar da kan al’umma aikace-aikacen hukumar.

Ya ce, a halin yanzu algus ya yi yawa a cikin kayayyakinmu musamman ma a bangaren kananan masana’antu da kuma kayayyakin da ake shigowa dasu daga kasashen waje wanda hakan yana cutar da al’umma saboda dadewar da suke.

Tun da farko da yake jawabinsa, babban jami’in hukumar kula da ingancin kayayyakin ta kasa Muhammad Alhaji Bukar ya ce sunje fadar ne dan su gabatar da kansu tare da sanar da Mai Martaba Sarki aikin hukumar ya shafi kamfanoni masu zaman kansu da gidajen Biredi da kuma sauran kayayyakin tande-tande.

Muhammad Alhaji Bukar ya tabbatarwa da Mai Martaba Sarki zasu yi aiki tsakaninsu da Allah domin kawar da masu algus a sassan wannan jiha ta jigawa.

Exit mobile version