Daga: Umar Faruk Birnin-Kebbi
Masarautar Gwandu a karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya bada umurnin sanarwar Dakatar da Wazirin Gwandu Alhaji Abdullahi Umar.
Sanarwar tana kumshe ne a cikin wata takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai a Birnin-Kebbi da ke dauke da sanya hannun sakataren Masarautar ta Gwandu Alhaji Musa Usman Bashar, a cewar takardar an dakatar da Alhaji Abdullahi Umar Waziri ne Saboda ya rubatawa Usman Dalhatu Zaria a ranar 9 ga watan Fabrairu na shekara ta 2021 da kuma wasu biyu zuwa ga sakataren Masarautar ta Gwandu duk a ranar ta 9 ga watan na Fabbrairu na shekara da muke cikin.
Haka kuma takardar ta kara da cewa an dakatar da Alhaji Abdullahi Umar, Wazirin Gwandu da ba a bayyana wa’adin lokaci ba.