Rabiu Ali Indabawa" />

Masarautar Japan Na Gaf Da Shiga Sabon Babi

Gwamnatin Japan ta bayyana sauya tushen sunan kasaitacciyar sarautar kasar da ta shafe sama da shekara 1000 tana wanzuwa.

A karon Farko dai Gwamnatin ta Japan, ta zabo “Reiwa”, wato sunan sarautar daga harshe ko adabinta, a maimakon na Kasar Chana da ta shafe shekara da shekaru tana amfani da shi. Daga ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa, lokacin da Yarima mai Jiran Gado Naruhito zai karbi mulki daga hannun Mahaifinsa Sarkin Japan Akihito, sunan sabuwar sarautar Kasar, wato “Reiwa” zai soma aiki.

Ma’anar sunan sarautar na “Reiwa” dai shi ne Abu mai kyau da kuma zaman lafiya. Karon na farko kenan da aka samu irin wannan sauyi a Kasar ta Japan a karkashin mulkin Firayin Minista Shinzo Abe, kasancewar sama da shekaru 1,300 kenan da Japan ta ari tsarin mulkin Sarautar gargajiya ta fuskokin suna da kuma Kalanda daga Kasar Chana.

A tsawon shekarun na baya, Japan ta yi amfani da sunaye kashi hudu kan sarautar gargajiyar Kasar da suka hada da Maiji, Taisho, Showa sai kuma Heisei, wato kokarin samar da zaman lafiya, wanda yanzu ake kan amfani da shi, amma daga ranar 30 ga watan Afrilu da muke ciki, za’a maye gurbin sunan sarautar da “Reiwa”.

Exit mobile version