Connect with us

TATTAUNAWA

Masarautar Jere Ta Yi Gagarumin Bikin Nade-Naden Sarauta

Published

on

A makon da ya gabata, Garin Jere da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ya dau ado da dimbin al’umma daga kusan ko ina na kasar nan wadanda suka yi dafifi domin shaida gagaruman nade-naden sarauta da masarautar ta yi. Abokan aikinmu na musamman, KHIDIR IBRAHIM da ABUBAKAR RABI’U sun tattaro mana bayanan sarautun da aka nada tare da takaitacciyar tattaunawa da wadanda aka yi wa: Ga yadda hirar ta kasance da su daya bayan daya:

 

Danmajen Jere, Alhaji Bashir Isah

Da farko, masu karatu za su so ka bayyana musu ma’anar Sarautar Danmaje a Masarautar Jere?           

Danmaje sarauta ce da ake nada dan sarki. Sarautar tana dauke da wasu ayyuka na fada. Tun daga tsaro zuwa abubuwa na tattalin arzikin masarauta.

 

Yaya kake ji a ranka kasancewar an wayi gari yau kai ne Danmajen Jere?

Farin cikina ba zai misaltu ba kan wannan sarauta da aka yi mana. Idan na duba yadda al’amarin ya faro har zuwa yanzu da muke tattaunawa da ku, sai in ji cewa farin cikin da nake ciki bai da iyaka. Kuma ga shi mun samu kyakkyawan shaida daga wurin jama’a wadanda suke bayyana cewa hakika an ajiye sarautar Danmaje a wurin da ta fi dacewa. Muna rokon Allah ya yi mana jagoranci. Ina kara godiya ga Allah bisa ni’imominsa. Ina kuma godiya ga daukacin wadanda suka halarta, babu abin da zan ce musu sai dai Allah ya bar zumunci. Galibin mutanen da suka zo ina da kyakkyawan alaka da su, ba na raina kowa duk irin matsayin da mutum yake kai nakan girmama shi.

 

Alamu na nuna Masarautar Jere ta bude sabon babi na nada hazikan ‘ya’yanta sarautu domin samun cigaba, a matsayinka na Danmaje, me za ka taimaka da shi wurin habaka cigaban masarautar da al’ummarta baki daya?

Komai yana tafiya da zamani. Sannan dukkan jagoranci irin wannan yana bukatar gogewar zamani. Ni da sauran wadanda aka nada mu mun yi karatu da tafiye-tafiye zuwa wurare daban-daban. Muna hulda da mutane daban-daban, muna ganin irin yadda masarautu ke tafiyar da harkokinsu na cigaba a zamanance. Za mu yi amfani da basirar da muka samu daga hakan wurin kawo wa Masarautar Jere cigaba. Za mu yi nazarin tsare-tsaren da ake kai a halin yanzu, abin da ya kamata a shigar za mu fada, wanda ya kamata a jefar za mu ba da shawarar a jefar tare da kawo hujjoji da dalilai masu karfi kan hakan.

Za mu kawo mutanen da za su kafa abubuwan cigaban gari domin matasa su samu aikin yi. Mun san wasu a Legas da Warri can Fatakwal da ke harkar mai. Idan mun ce musu su zo nan sai su nuna akwai matsalar tsaro bisa irin abubuwan da suka faru a baya. Amma alhamdulillahi ga shi yanzu an samu tsaro saboda yadda gwamnati ta mike tsaye abin ya ragu sosai in ma ba a ce an kawar da shi ba baki daya. Za mu sanar da su cewa komai ya daidaita, sannan su ma za su sanar da wasu. Da haka za su zo su kafa masana’antu da gonakai na zamani da za su bunkasa tattalin arzikin wannan yanki. Za mu karfafa gwiwar matasa su tashi tsaye su zamo masu dogaro da kansu cikin yardar Allah.

 

Me kuke da bukata daga al’ummar gari kan wannan kudirin naku na kawo cigaba?

Da farko muna so su fahimci alfanun abubuwan da muke son kawowa na cigaba tare da ba mu goyon baya a kai dari bisa dari. Idan muka samu wannan daga gare su, za mu samu nasarar abubuwan da muke son aiwatarwa.

 

Matasa a wannan zamanin da dama sun fada harkar shaye-shayen miyagun kayan maye da sace-sace, ko me Danmaje zai taimaka da shi wurin shawo kan wannan matsala a cikin al’ummar Jere?

Tabbas yana daya daga cikin abubuwan da suke bakanta mana rai. Shaye-shaye na matukar bata tarbiyya. Idan mutum yana yi zai tsunduma sace-sacen kayan jama’a. Tun suna yi a boye har za su fito fili, idan ma ba tashi tsaye aka yi ba sai su fara daukar makamai suna bin gidajen jama’a. Da yardar Allah muna da yakinin cewa ba da jimawa ba za mu tinkari wannan matsalar a masarautar nan domin magancewa. Musamman ni kaina ina da wasu tsare-tsare masu karfi da dabarbarun da ‘yan kudancin Nijeriya suke amfani da su a kan matasa masu shaye-shaye da sace-sace. Cikin yardar Allah zan gabatar wa masarauta da su wanda idan an aiwatar, ko a wajen gida mutum ya ajiye kayansa zai zo ya tarad da shi yadda ya ajiye kamar yadda Jerenmu take a da. Ina da kyakkyawan tsari a kan haka. Sannan za mu jawo masu yi a jiki tare da nuna musu illolin abin da suke yi. Idan mun yi wannan wadanda suka shiryu za mu ji dadi tare da yaba musu. Wadanda suka kekashe kuma akwai hanyar da su ma za a bi da su wurin tsugunar da su a wani wuri na musamman da za a kula da su bisa yadda doka ta yi tanadi.

Barden Jere, Alhaji Ibrahim Isma’il

 

Allah shi taimake ka an nada ka sarautar Barden Jere, ko me wannan sarautar take nufi a Masarautar Jere?

A uzu billhi minas shaidanir rajim, bismiallahir rahmanir Rahim. Sarautar gargajiya ta Barde, wadansu masarautun sukan ce Barade, wasu masarautun sukan ce Barde, ana nufin jarumi, wato kamar wanda shi yake shugabantar yaki; kwamanda ke nan, wannan ita ce ma’anar Barde ko Barade.

 

Allah ya taimaki Barde, me za ka ce dangane da wannan ranar?

Alhamdulillahi ka san abu ne wanda ya zo na gadon mahaifinmu, Allah yajikansa ya rasu shekaru kusan goma sha da suka wuce, sai yau Allah cikin hikimarsa da ni’imarsa ya sa aka tabbatar da sarautar aka ba mu. Ka ga farin ciki kuwa Alhamdilillahi da wannan ni’ima da Allah ya yi. Ina cikin farin ciki kwarai-kwarai da gaske, mutum ya gaji mahaifinsa a rayuwarsa ,jama’arsa da iyaye sun ce wane mtumin arziki ne a ma sa masarauta, ka ga kuwa wannan ba karamin abin arziki ba ne.

 

Mutane sun zo daga wurare daban-daban wane irin sako za ka aika musu da shi?

To alhamdulillahi wannan ya nuna ana zaman lafiya da mutane, kamar yada suka zo daga wurare daban-daban. Babban abin da ya bani sha’awa shi ne,  Shugabata wadda muke aiki tare da ita wato Shugabar ma’aikatan Jihar Kaduna ta samu lokaci ta ziyarci wannan lamari. Sakon da nake son mika musu shi ne, na gode musu da wannan zumunci kuma Allah ya saka musu da alheri, Allah ya bar zumunci.

 

A matsayinka na sabon Barden Jere, wane irin cigaba kake ganin masarautar Jere za ta samu daga gare ka?

To Alhamdulillahi, wato ka san Jere gari ne da yake bunkasa kwarai da gaske, saboda haka akwai bukatar a zauna a jajirce a kalli abubuwa a shirya, sannan a kawo ayyuka na cigaba a masarauta, ayyukan da za su kawo cigaban arziki, zaman lafiya da zamantakewa, in sha Allahu za mu shigo ciki. Kuma kamar yadda suke zaton za mu ba da shawara ta aikin alheri, insha Allahu za mu yi. ina kiran dukkan wadanda aka yi wa sarauta yau ba ni kadai ba da wadanda muka samu a ciki, mu zo muka wo ayyuka na cigaba da zamnatakewa, zaman lafiya da cigaban addininmu a garin Jere da jihar Kaduna baki daya.

 

Dandarman Jere, Hon. Musa Rayyan

Allah ya taimake ka an yi saruata, ko me ake nufi da Dandarma?

Dandarman Jere dai sarauta ce da muka ara daga ainihin masarautu da dama a kasara Hausa. Kusan za a iya cewa duk wata babbar masarauta akwai wannan sarauta. Sarautar ta Dandarma sarauta ce babba, domin akwai abokina da yake da wannan sarauta dan marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, wanda mun yi makarantar kwalejin Barewa ta Zariya da shi. Yanzu haka shi ne Dandarman Kano, Hakimin Kura, wato Bello Ado Bayero.

 

Wane irin farin cikin sabon Dandarman Jere zai nuna?

To Alhamdulillahi, farin cikina a yau, farin cikina bai da iyaka, domin ‘yan uwa sun nuna mana zumunci da ‘yan uwantaka. Tun da ake nadin sarauta ban yi tsammanin an samu taro kamar wannan a garin nan ba. To farin cikina gaskiya bai da iyaka. Kuma muna mika godiyarmu ga Allah madaukakin Sarki da ya nuna mana wannan rana, kuma babbar rana ce a gare mu ta tarihi wadda ba za mu mance da ita ba.

 

Wadanda suka zo daga nesa da na kusa, wane sako Dandarma yake da shi gare su?

To Alhamdulillahi, baki da suka zo don su taya mu murnar wannan mukami da Allah ya ba mu, wadansu ma duk sun kokkoma gidajensu, wasu kuma suna kan hanya, to fatanmu dai yadda suka zo lafiya Allah ya mayar da su gidajensu lafiya,kuma Allah ya saka musu da alkhairi kan zumuncin da suka yi mana.

 

Akwai alamun marautar Jere na sabon zubi wajen daukar gogaggu a harkokin rayuwa tana nada su sarauta, me Dandarman Jere ke da shi sabo da zai kawo wa masarauta cigaba da kuma al’ummar gari?

To akwai abubuwa da dama wadanda muna son mu da muka zo sababbi, mu yi kokari mu ga cewa an samu canji a wannan masarauta a fannoni da dama, fannin ilimi, fannin kiwon lafiya, koda yake muna da kungiyoyi da yawa a garin nan, haka suke zaune babu tsari, muna fatan a wannan shigowa tamu za mu kafa kwamiti a karkashin wannan masarauta, wato Jere Traditional Council mu samun kwamiti na kiwon lafiya, kwamitin ilimi da na ainihin kula da kungiyoyi da sauransu.

Ta wannan kungiyoyi za su samu hadin gwiwa da su, don dai a san yadda za a yi wannan gari ya samu cigaba, kuma Alhamdulillahi wannan garin tun da muna kusa da Abuja, Allah ya taimake mu; ga abubuwa nan na cigaba ba su da iyaka. To muna fatan in Allahu muna fatan shigowarmu zai zama alkhairi.

Salenken Jere, Alhaji Hamza Yakubu

 

Allah ya taimake ka, me ake nufi da Salenken Jere?

Salenke sarauta ce ta ‘Chief Confidential Officer (Babban jami’in sirri) na mai martaba sarki. Salenke yana da rawar da yake takawa kafin ma majalisar sarki, shi ne zai je ya zauna ya tattauna da mai martaba Sarki a kan abubuwan da za a zartar, to shi salenke ne ke fara furta wa majalisa abin da sarki yake bukata a yi.

 Za mu kawo mutanen da za su kafa abubuwan cigaban gari domin matasa su samu aikin yi. Mun san wasu a Legas da Warri can Fatakwal da ke harkar mai. Idan mun ce musu su zo nan sai su nuna akwai matsalar tsaro bisa irin abubuwan da suka faru a baya. Amma alhamdulillahi ga shi yanzu an samu tsaro saboda yadda gwamnati ta mike tsaye abin ya ragu sosai in ma ba a ce an kawar da shi ba baki daya

 

Me za ka ce dangane da wannan rana da aka yi muku nadi?

A gaskiya farin ciki ba a iya fada, tun da gaskiya tun da ka rayu Allah ya kadarta abu a kanka to sai dai ka gode wa Allah, domin duk abin da aka ce wani abu na farin ciki zai same ka na alkhairi, to babu shakka akwai kalubale, amma sai ka ga ya zo kamar an yi ruwa an dauke, wannan al’amari an yi kuma tsakanina da Allah  na yi imani har ga Allah daga Ubangiji ne, in Allah ya yar da za mu yi aiki tukuru, za mu ba da hadin kai da duk yaddaza a yi mu ga wannan gari ya cigaba in Allah ya so ya yarda.

 

Mutane sun zo daga wurare don taya ku farin ciki da goyon baya, me za k ace musu?

A gaskiya duk wanda ya zo daga nesa zuwa kusa wannan gari zuwa wannan sarauta, Allah ya yi musu albarka, Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.

 

A matsayin ka na sabon Salenken Jere, me za ka yi wanda zai sa garin da al’ummarsa su amfana?

Haka ne, to ita dai ma’anar sarauta ana nufin ihsani, ma’anar sarauta buda hannu ne, ma’anar sarauta taimakawa. Muna rokon Allah mu da Allah ya nufe mu da samun wannan sarauta za mu hada kanmu, duk wata matsala da za a samu a wannan gari, daga yara zuwa manya Allah zai ba mu ikon daukar nauyi iya gwargwadon abin da za mu iya, don ciyar da wannan kasa ta mu gaba in Allah ya yarda. Aiki za mu yi tukuru, don sha’awar da aka yi kenan a gare mu aka ba da sarautar, ai da can ba haka sarautar take ba, sarautar daga biyu ce sai uku, daga Dallatu ne sai waziri sai shamaki, daga shamaki sai sarkin fada, daga sarkin fada sai turaki, su kenan, amma yanzu muna da sarautu sun fi goma sha, to ka ga a nan ai an sake samun cigaba.

 

Walin Jere, Alhaji Isah

Ranka shi dade Masarautar Jere ta nada ka a matsayin Walin Jere, ko za ka bayyana wa masu karatu me Sarautar Wali take nufi?

To, kamar dai yadda muka samu tarihi, a da can-can kafin zuwan Turawa su rarrage abubuwan da ake yi na tafiyar da sha’anin kasa a hannun masarautu, Wali shi ne yake kula da rabon duk wasu abubuwa da suka safi arzikin kasa. Shi ne zai ce ga yadda za a yi; ga yada za a yi wurin tafiyar da dukiyar kasa. Wannan shi ne a takaice bisa fahimtarmu.

 

Yaya kake ji a ranka dangane da wannan sarauta da aka nada ka?

Alhamdulillah, ina nuna farin cikina ga Allah Madaukakin Sarki da ya kawo mu wannan rana. Kusan zan iya cewa ikon Allah ne ya sa a rayuwata za a wayi gari an nada ni a wannan sarauta. Ina kuma gode wa saraun jama’a musamman Masarautar Jere da ta amince da mu ta nada mu wannan sarauta. A da, da farko mai girma Hakimin Jere Alhaji Yusuf ya nada ni ne a matsayin mai unguwar fada. Cikin ikon Allah, da yake ina halartar taro a masarauta kuma ina ba da gudunmawa wajen ba da shawarwari da sauransu, sai shi Hakimin ya sake cewa in yi nazari tare da rubuta neman wata sarauta da za ta sa in kasance a cikin majalisar Masarautar Jere baki daya. Kuma ga shi Allah ya tabbatar da haka, alhamdulillahi. Muna godiya ga dukkan wadanda suka halarta, Allah ya saka wa kowa da alkhairi ya sa an koma gida lafiya.

 

Akwai alamun Masarautar Jere tana sabon zubi wajen zakulo matasa masu hazaka ga ciyar da al’umma gaba, a matsayinka na sabon Wali, wace gudunmawa za ka bayar ga cigaban al’ummar wannan masarauta?

Zan iya cewa tun kafin nada ni wannan sarauta ta Walin Jere, ina baiwa masautar Jere gudunmawa musamman ta fuskar sana’ar da nike yi ta filaye da safiyo. Muna sayan fili a daji mu yayyanka (abin da Turawa ke ce wa layout) mu fitar da tsarin gidaje da hanyoyi da sauransu. Ta wannan harkar ina kawo wa garin Jere cigaba ta hanyar bunkasa fadinta. Kuma zan cigaba da yin hakan domin kara samun jama’a masu kawo wa gari cigaba da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: