Connect with us

RAHOTANNI

Masarautar Kano Da Kamfanin Bizi Mobile Sun Shirya Gudanar Da Agency Banki Irinsa Na Farko

Published

on

Masarautar kano karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin kano, Malam Muhammadu Sunusi II, da hadin gwiwar Kamfanin Bizi mobile Cashless Consultant limited, sun shirya gudanar da taron bita na musamman a kan hada-hadar kudi irin na zamani, wanda a turance ake kira da “sensitazation on Agency and banking fair”, wanda aka shirya musamman domin Hakimai da Dagatai da masu rike da sarautun Jihar kano baki daya.

A wata takarda sanarwa wacce ta sami sa hannun Shugaban rukunonin kamfanin Bizi mobile, Alhaji Aminu Bizi, wacce aka rabawa manema labarai a kaduna, ya bayyana cewa, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II, ya amince da kamfanin Bizi mobile da su shirya taron bita na musamman domin wayarwa Hakimai da Dagatai, da duk masu rike da sarautar gargajiya na jihar kano, da kai a kan mu’amala da hada hadar kudi irin ta zamani,wato “Cashless policy and Agency banking”, wanda wannan tsari, Mai Martaba ne da kansa ya bullo da shi, a lokacin da yake rike da mukamin Gwamnan babban bankin Nijeriya, wato CBN, domin rage ma Al’umma wahalhalun mu’amala da kudade a hannunsu.

A cewarsa, wannan shi ne karo na farko da aka taba shirya irin wannan biki, wato wanda a turance ake kira da first Agency banking fair 2018, tare da hadin gwiwar Mai Martaba Sarkin Kano, domin cinma muradin karnin hada hadar kudi irin na zamani, wanda akayi ma lakabi da bision 2020, wanda kamfanoni da bankuna zasu sami damar baje hajarsu ta hanyar bude asusun ajiya na bankuna kai tsaye.

Sannan a yayin wannan bikin na agancy banking fair, Al’umma zasu sami damar zuwa domin a bude musu asusun ajiya na bankuna, sannan a yi maka katin ATM da BBN nan take ba tare da jeka ka dawo ba.

Daga karshe, Shugaban kamfanin Bizi mobile, Alhaji Aminu Bizi, ya yi kira ga kamfamonin da bankuna, da manya da kananan ‘yan kasuwa da cewa, ga fa dama ta samu wanda za su zo domin baje hajarsu kai tsaye ga Al’umma, domin wannan biki na “Agency banking fair” shi ne, irinsa na farko da aka taba yi a tarihin jihar Kano baki daya.

Sannan ya gode ma Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, a bisa wannan dama da ya bai wa al’ummar jihar Kano, wanda a cewarsa, wannan ba karamin ci gaba ba ne ya kawo ma jihar Kano da al’ummarta baki daya.

A wata takarda da Masarautar kano ta fitar wacce ta sami sa hannun Sakataren Masarautar, Alhaji Mahmoud Aminu Bayero, a madadin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II, ya bayyana matukar farin cikinsa dangane da wannan bita akan hada hadar kudi, da kamfanin Bizi Mobile zai gudanar na tsawon kwana bakwai,  ga masu da rike da sarautun jihar Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II, ya kuma umurci Sarkin Shanun kano, kuma Hakimin  Rimin Gado, Alhaji Shehu Muhammad Dankai, da ya wakilce shi a yayin bude wannan taron bita na tsawon kwanaki bakwai. Taron wanda aka shirya gudanar da shi ranar 17/9/2018, idan Allah ya kai mu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: