Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Masarautar Karaye ta sha alwashin sake buga littafin Tarihin Fulani wanda lardin Arewa suka buga tun a Shekara ta 1963.
Shawarar daukar nauyin sake buga littafin ta biyo bayan la’akari da muhimmacin littafin a tarihin Daular Sokoto, dalibai da kuma sauran al’ummar Musulmi baki daya. Littafin wanda ya bayyana asalin tarihin Fulani da muhimmancinsu.
Haka kuma daga cikin abububawan da littafin ya kunsa, harda ainihin yadda Jihadin Shehu Usman Bin Fodio ya faro da kuma tarihin khalifofi Sarakuna daga Shehu Usman dan Fodio har zuwa mai alfarma Sarkin Musilmi Abubakar III.
Farfesa Sambo Wali Junaidu ya bayyana wannan kyakkyawan yunkuri, inda ya jaddada farin cikin masarautar ta Sokoto ga Sarkin na Karaye Dr. Ababakar II, kamar yadda jami’in yada labaran masarautar Karaye Haruna Gunduwawa ya shaidawa LEADERSHIP A Yau.