Connect with us

LABARAI

Masarautar Katsina Ta Yi Sabon Madugu

Published

on

Abdulmuminu Kabir Usman, ya amince da nada Shugaban Ma’aikatan Fadar Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Muntari Lawal, a matsayin sabon Madugun Katsina.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin wata takarda, wacce sarkin ya sanya wa hannu, inda ta nuna amincewarsa ga ba wa Shugaban Ma’aikatan sarautar.

A cikin jawabin Sarkin ya nuna cewa, “kamar yadda ka rubuto takardar neman a nada ka, to na amince kuma nan gaba kadan za a sanya ranar bikin nadin.”

Daga sai sarkin ya taya shi murnar da addu’ar fatan Alheri.

Shi ma sabon Madugun Katsina ya nuna jin dadinsa bisa ga wannan karamci da Majalisar Masarautar Katsina ta yi ma sa na amincewa da a ba shi wannan sarauta, ya na mai cewa, “Ina mika dimbin godiyata.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: