Masarautar Minna Ta Dakatar Da Hawan Sallah

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Masarautar Minna ta shelanta cewar ta soke hawan sallah karama a fadin masarautar. Bayanin da wakilin ya samu shi ne masarautar tace duba da halin rashin tsaro da ake fuskanta kuma an koro daruruwan mutane daga gidajen su sun watsu cikin gari dan neman mafaka, bai yiwuwa cikin irin wannan wannan yanayin a tunkari wani abu da sunan bukin sallah.

Alhaji Yusuf Tanko Kuta ( Kimiyyan Sarkin Minna) yace mai martaba sarkin Minna Alhaji Umar Faruk Bahago ya damu gaya da halin da jama’ar masarautar ke ciki musamman mutanen karkara da aka watsa su suna neman matsunni da abinda za su ci, dan haka masarautar ta dakatar da hawan sallah a fadin masarautar kuma ta nemi jama’a da su yi anfani da sauran kwanakin Ramadan wajen ganin Allah ya kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga ga al’ummar karkara.

Masarautar ta yabawa al’ummar bisa juriya da jajircewa wajen hakuri da halin da suke ciki, tace masarautar da gwamnatin jiha ba bacci suke yi ba wajen daukar matakan da suka dace dan ganin an kawo karshen rashin tsaro a masarautar da jihar Neja da kasa baki daya.

Exit mobile version