DAKTA ABUBAKAR ABDULLAHI MARAFA (Iyan Deba) A tattaunawarsa da LEADERSHIP A Yau Asabar, ya bayyana Masarautar yankin Yemaltu Deba a matsayin wadda da ta fi kowace Masarauta dimbin tarihi da son zaman lafiya a fadin Jihar Gombe. Sannan ya yi karin haske akan wasu bayanai daban. Ga yadda ta kasance;
Ranka ya dade, muna taya ka murnar sabon nadin da aka yi maka, za mu so mu jin ya aka samu wannan rawani?
Alhamdulillah! Kamar yadda al’umma suka sani, shi mulki ko sarauta abu ne na Allah, wanda yake bayarwa ga wanda ya so. Ban taba tunanin zan samu wannan sarauta ba, amma cikin ikon Allah, lokacin babanmu mai rasuwa ya dauki sarautan Iyan Deba ya bani, ba don komai ba, sai don yadda yake ganin kokarinmu da kuma jajircewanmu wajen kawoma al’ummarmu da jiharmu ta Gombe abubuwa wadanda za su amfani mutane. Gaskiya na ji dadi, na yi matukar farin ciki wanda ba zan iya misalta shi ba.
Kasancewarka likita wanda ya kware a fannin maganin gargajiya, ga shi kuma kana yawan tafya kasashen waje, ta yaya za ka gudanar da wadannan abubuwa a lokaci guda?
Don haka gaskiya wannan sarautar da na samu ta karamun kwarin gwiwa wajen taimakawa jama’a.
A kwanakin baya ne Allah ya yi wa mai Martaba Sarkin Deba rasuwa, kuma a halin yanzu har an nada wani sabon Sarki. Shin ya za ka kwatanta tsohon sarki da kuma wannan sabon Sarkin?
Alhamdulillah, muna addu’ar Allah ya ji kan babanmu mai Martaba Sarki, Ubangiji ya yi masa rahama.
Wannan sabon Sarki da aka nada muna masa addu’a, Ubangiji Allah ya kara masa hikima da basira da Ilhama ta yadda zai kawoma Masarautar Deba abubuwan ci gaba. Da wancan sarki da wannan Sarkin duka idan ka duba mutane ne masu son jama’a, ko da yake dama shi Sarki Baban kowa ne, amma tasu dangantakar da mutane ta daban ce, kuma mu din da aka ba mu sarauta a Masarautan nan an ba mu ne a ga irin rawar da za mu iya takawa wajen kawo zaman lafiya da taimakama matasa. Watau mu ga matasa sun samu ilmi, aikin yi, hakan kuma ba wai yana nufin mun manta da dattawa ba ne, su ma muna tare da su.
Maganar nan ma da muke yi yanzu haka, ka ga akwai kokarin da nake yi na wani kamfani Manash Global Inbestiment Limited, wanda muna magana yanzu haka da Kasar Afirka ta Kudu, Uganda da kuma sauran wasu Kasashen Duniya, wanda muna kokari mu ga mun zo har nan cikin garin Deba domim mu mu kafa kamfani, wanda zai samawa matasanmu da jama’armu ayyukan yi, musamman da muka ji shi wannan sabon Sarki mutum ne wanda yake da kishin al’ummansa, kuma yake so ya ga al’umma sun zauna lafiya, don muna jin kiraye-kiraye da yake yi musamman akan abin da ya shafi harkar ilmi da tarbiya; yadda iyaye za su kula da ‘ya’yan su, saboda haka ne ma daga lokacin da aka bani sarauta a garin Deba mun dauki yara kusan 40 daga Firamari har zuwa Sakandire, kuma wannan muna fada ne domin Allah ba wai domin riya ba.
A cikin garin Gombe akwai makaranta da aka bude ana koyar da sana’o’i irin su man shafawa, turare, dinki da duk mutumin da yaje ya bincika a wurin zai samu cewa lallai Dan Iyan Deba ya dibi Mata dari biyu (200), wanda kuma an basu horo an koyar da su sana’o’i ba domin komai ba, sai don yadda za su dogaro da kansu.
Gaskiya wannan Sabon Sarki da ya zo ya sosa mana inda yake mana kaikayi ne, domin babu wata al’umma da za ta ci gaba ba tare da ilimi ba, babu wata al’umma da za ta ci gaba ba tare da zaman lafiya ba, don haka muna neman hadin kan al’umma da goyon bayansu. Sai mun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ne kamfanonin za su zo su zuba hannayen jari.
To, Alhammdulillah. Kamar yadda jama’a suka sani, Garin Deba yana da dinbin tarihi dadadde, kuma yana da mutane wadanda suke da kishi da hadin kai, ga kuma son zaman lafiya. Ko a wannan Baban Sallar ma da ta wuce sai da mai Martaba Sarki ya yi kira tun daga kan Dagatai zuwa masu Unguwanni dama duk sauran al’umman gari kowa yana da hakki, saboda kowa in ya gyara gidansa, sai mu ce unguwa ta gyaru, idan unguwanni suka gyaru to, garuruwa sun gyaru, idan kuma garuruwa suka gyaru to, sai mu ce kasanmu Nijeriya ta gyaru; idan Kasashen suka gyaru to, sai mu ce gaba daya Duniya ta gyaru. Ko kaima za ka iya ganin wannan garin ya sha bamban da irin garuwan da ka ke zuwa idan dai akan maganar zaman lafiya ne, domin ina mai tabbatar maka da cewa ba alfahari ba, duk Masarautun dake Jihar Gombe, babu Masarautar da ta kai Deba son zaman lafiya.
Wace shawara ka ke da ita ga takwarorinka masu rike da mukaman Sarauta?
Kiran da nake da shi, shi ne, duk abin da dan adam zai yi to ya yi shi da gaskiya da kuma rikon amana. Wannan gari namu ba mu da wani gari da ya wuce shi, domin a nan aka haife mu, a nan iyayenmu suke, a nan muka girma, idan da a ce ina da dama to da zan iya zamar da wannan gari namu ya zama kamar Birnin Landan ko Saudiyya, kai ko ma Dubai. Saboda haka babban kiran da zan yi a garemu shi ne, mu zo mu hada kai, domin mu samarwa jama’armu zaman lafiya da kuma ci gaba, mu gane cewa hannu daya baya daukan jinga.
Akwai wadanda ka yi takara da su wajen neman wannan sarauta, wane kira za ka yi gare su bayan nasarar da ka samu?
Dukkanin wadanda suka nemi Sarautar ba su samu ba, ba su da wani ja, domin mutane ne masu Ilimi, wanda kuma sun yarda da kaddara, sun san cewa mulki na Allah ne, yana bada wa ne ga wanda yake so a lokacin da ya so, kuma sun san cewa wannan yin Allah ne. na san dukansu a shirye suke domin su goya wa wannan Sarkinmu baya, domin kowa na da gudunmuwar da zai iya bayarwa.
A karshe me za ka ce ga masoyanka wadanda suka nuna goyon baya game da wannan nadin da aka yi maka?
Ni Dakta Abubakar Abdullahi Iyan Deba, ina mai jinjina ga masoyana gaba daya, kuma Insha Allah zan kara sadaukar masu da lokacina wajen yi masu hidima.
Zan yi amfani da wannan damar wurin ba dimbin masoyana wadan da ban samu damar aika masu da sanarwar nadin ba da su yi hakuri, abinda kawai nake so daga gare su shi ne su ci gaba da sanya ni cikin addu’o’insu kan Allah Ubangiji ya kara mana juriya da hakuri, ya sa duk abin da za mu yi ya zama akwai bisa doron gaskiya da rikon amana.
Babban abin alfaharina shi ne in ga na yi wani abu a duniya wanda jama’a za su rika amfana da shi, wanda kuma zai sa su rika yi min addu’a ko bayan raina.