Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Masari Ga Jami’an Kwastam: Ku Guji Kashe Jama’a A Cikin Katsina

by
3 years ago
in LABARAI
2 min read
Kungiyar Likitoci Reshen Jihar Katsina Ta Karrama Wasu Fitattun Mutane
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya gargadi jami’an hukumar hana fasa kwabri ta kasa kan yadda suke haddasa rasa rayukan jama’a a lokacin gudanar da aikinsu a jihar Katsina

Gwamna Masari ya ce ya kamata jami’an su lalubo wata hanyar ta daban wanda za su mutunta dangantakar da ke tsakaninsu da al’ummomin da ke zaune kusa da kan iyakoki da kuma cikin gari domin kauce wa kisan ba gaira ba dalili

Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tagawar mai kula da ayyuka na musamman a kan iyakokin Najeriya a jihar Katsina (National Border Drill Operation), Mataimakin shugaban Hukumar ta Kwastam, ACG Bashir Abubakar tare da sauran ‘yan tagawarsa a ofishinsa da ke gidan gwamnatin Katsina

Labarai Masu Nasaba

Zargin Sauyin Sheka Yasa Majalisar Dokokin Kano Ta Dage Zamanta Na Ranar Litinin

Deborah: Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bukaci A Zauna Lafiya

Haka kuma Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa ta ba da fifiko wajan  kare rayuka da dukiyoyin al’umma ne saboda haka ba za su laminci kisan ba gaira ba dalili ba daga jami’an hukumar hana fasa kwabri ta kasa ba a lokcin gudanar da aikinsu.

“Ina tunanin ya kamata su zama kamar fararan hula wajan tafiyar da aikin da doka ta baku damar yin, yin amfani da harbin bindiga acikin birni  ba abu da zamu laminta ba, komi zaku yi, ku yi shi can cikin da ji, ko kuma akan iyakoki” inji Masari

“Za mu cigaba da ba da duk wata gudunmawa da kuke bukata a ya yin wannan aikin naku, abinda kawai muke so daga wajanku shi ne ku daina yin harbe-harbe a cikin garin wanda hakan yana haifar da razani da tsoro ga jama’a, saboda hakan yana san jama’a su rika gudu a ya yin da wasu ke samun munanan raunuka wasu kuma suna rasa ransu.” In ji shi.

Gwaman Masari wanda ya jaddada cewa idan suka shiga cikin gari yin aikinsu su kaucewa dabi’ar nuna karfin bindiga a kan jama’a, abinda ake tsoro karar bindiga kuma hakan shi zai fi saukin wajan gudunar da aikin tare da samun nasarar da ake bukata.

Kazalika Gwamna Aminu Masari ya yi kira ga tawagar da su sanya sarakuna gargarjiya da shuwagabannin addini wajan tafiyar da wannan aikin na hana fasa kwabri da sauran ayyukan a jihar Katsina da kuma kasa baki daya

Tunda farko da yake nasa jawabin shugaban tawagar ayyukan na musamman a kan iyakokin Nijeriya ACG Bashir Abubakar ya ce an kawo wannan tawaga tasu ce domin su samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin ‘Yan Nijeriya da kuma dawo da martabar tattalinz arziki kasa ta hanyar ba da kariya a kan iyakokin ta kasa da masana’antu

Ya ce ya zuwa yanzu sun samu nasarar kama motoci 288 ta tare buhunan shinkafa ‘ya kasar wajen mai yawa da sauran abubuwan da aka shigowa da su, sai ya yi kira ga gwamna Masari ya ba su goyan bayan domin gudanar da wannan aiki na su yadda ya kamata

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

NIS Ta Kaddamar Da Shalkwatarta A Akwa Ibom Da Ta Gina Cikin Wata Shida

Next Post

Gwamna Ganduje Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2020 Na Sama Da Naira Biliyan 197

Labarai Masu Nasaba

Zargin Sauyin Sheka Yasa Majalisar Dokokin Kano Ta Dage Zamanta Na Ranar Litinin

Zargin Sauyin Sheka Yasa Majalisar Dokokin Kano Ta Dage Zamanta Na Ranar Litinin

by
12 hours ago
0

...

Deborah: Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bukaci A Zauna Lafiya

Deborah: Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bukaci A Zauna Lafiya

by
15 hours ago
0

...

Ganduje Ya Umurci Bala Ya Kula Da Ofishin Shugaban Ma’aikata Fadar Gwamnatin Kano

Ganduje Ya Umurci Bala Ya Kula Da Ofishin Shugaban Ma’aikata Fadar Gwamnatin Kano

by
20 hours ago
0

...

Deborah: Matasan Musulmai Ba Su Kona Min Gidana Ba —Bishop Kukah

Deborah: Matasan Musulmai Ba Su Kona Min Gidana Ba —Bishop Kukah

by Abubakar Abba
22 hours ago
0

...

Next Post

Gwamna Ganduje Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2020 Na Sama Da Naira Biliyan 197

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: