Masari Ya Bukaci Malaman Jami’o’i Da Su Janye Shirin Shiga Yin Yajin Aiki

Masari

Daga Sagir Abubakar,

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bukaci malaman jami’o’i da su guji shiga yajin aiki marasa amfani da zai raunata harkokin ilimi a manyan makarantu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbi bakuncin shuwagabannin kungiyar malaman kwalejin Hassan Usman Katsina karkashin jagorancin Dakta Sabi’u Ya’u wanda suka kawo masa ziyara.

Gwamna Masari ya lura da cewa malaman manyan makarantun suna shiga yajin aiki ne duk da cewa ba su da wata matsala da makarantunsu.

Ya tunasar da su a kan bukatar da ke akwai na cewa manyan makarantun da ke Jihar Katsina bai kamata su shiga yajin aiki ba sai in har batun ya shafi ci gaban manyan makarantu.

Ya taya murna ga shugabancin kungiyar malaman kwalejin game da yadda ake samun nasarar gudanar da harkokin karatu cikin kwanciyar hankali ba tare da korafi ba.

Gwamnan ya bukace su yi kyakkyawan amfani da lokacinsu domin fadada karatunsu a matsayinsu na wadanda suke gyara halayyar dalibai bayan iyaye.

Tun da farko dai, shugaban kungiyar malaman kwalejin Hassan Usman Katsina, Dakta Sabi’u Ya’u Abdullahi ya ce ziyarar na da nufin jajantawa a kan kalubalen tsaro da ake fama da shi a jiha da kuma kasa baki daya.

Ya ce malaman kwalejin sun damu matuka game da yanayin da ya hana wadanda ba ‘yan asalin jihar ba kara karatu a kwalejin.

Dakta Abdullahi ya nuna jin dadinsa game da kokarin Gwamnatin Masari na magance matsalar.

A cewarsa, ya sanya aka kara daukar yawan dalibai wadanda ba ‘yan asalin jihar ba a shekarar karatu ta bana.

Exit mobile version