Daga Sagir Abubakar, Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta bada tabbacin ɗaukar matakai domin kawo ƙarshen ƙaura da matasa su ke yi daga ƙauyuka zuwa birane. Alhaji Aminu Bello Masari ya bada tabbacin hakan ne a lokacin da yake jawabi ga wasu ƙungiyoyi ‘yan asalin jihar Katsina da su ke zaune a Abuja a masaukin gwamnatin Jihar Katsina da ke unguwar Asokoro. Gwamnan ya bayyana cewa daga cikin matakan sun haɗa da inganta noman rani da kuma tallafawa matasa da sauransu.
Alhaji Aminu Bello Masari ya jaddada buƙatar da a ke das hi ga matasa su dinga gudanar da rayuwa ta gari ganin cewa basu kusa da iyayensu Ya kuma buƙace su, da su kasance jakadu na gari na jihar kuma su guji aikata munanan laifuka.
Gwamnan ya buƙaci suyi amfani da abin da suke samu a wajen kasuwancinsu wajen ilimantar da ‘yayansu, ya kuma buƙace su da su guji yin amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaɗa kalaman ɓatanci a cikin al’umma.
A jawabinsa, mai magan da yawun ‘yan asalin jihar Katsina da ke zaune a Abuja Alhaji Yusha’u ya ce yawancin matasan suna gudanar da sana’o’i da su ke tafiyar da rayuwarsu da suka haɗa da tuƙa ‘yar ƙurƙura ɗinki da sauran ƙananan sana’o’i. ya kuma ba da tabbacin cewa ‘yan jihar Katsina ne mafi ƙarancin wajen aikata laifuka a babban birnin tarayya. Bisa la’akari da kulawar da gwamnatin Jihar Katsina na ganin kowane matashi ya samu abin yi ba abin kunya ba.
Shugaban ya ƙara kira ga matasa da su kasance masu kishin jihar su dama ƙasa baki ɗaya kamar yadda gwamnatin jihar ke kishinsu. Da ga nan ya yaba wa gwamna Aminu Bello Masari wajen kulawa da matasan jihar da kuma ba su ilimi yadda ya kamata.