Connect with us

WASANNI

Mascherano Ya Yi Ritaya Daga Bugawa Argentina Wasa

Published

on

Dan wasan tsakiya na Argentina Jabier Mascherano ya yi ritaya daga bugawa kasar kwallo bayan da aka fitar da su daga gasar kofin duniya a ranar Asabar din data gabata.
Dan kwallon mai shekara 34 ya bugawa kasar wasa sau 145, ciki har da wanda suka sha kashi a hannun Faransa da ci 4-3 a zagayen ‘yan kungiyoyi 16 na gasar a ranar Asabar.
Mascherano ya buga dukkan wasannin da Argentina ta yi a gasar ta Rasha – kuma ita ce ta hudu da ya halatta a jere a tarihi.
Ya shaidawa manema labarai cewa “Ni dai a wuri na, komai ya zo karshe domin Daga yanzu ni ma magoyin bayan Argentina ne kawai.”
Dan kwallon wanda ya lashe lambar zinare ta Olympic sau biyu, ya fara bugawa kasar wasa ne a 2003, kuma ya fara kwallo ne a kungiyar Riber Plate dake kasar Argentina.
Ya buga kwallo a kungiyoyin West Ham da Liberpool da kuma Barcelona sai dai a yanzu yana buga wasa ne a kasar Sin wato China tare da kungiyar Hebei China Fortune
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: