kungiya Masu samar da gyada, sarrafawa da kasuwancinta na Nijeriya sun yi kira ga membobin kungiya da sauran jama’a da su yi watsi da wasu da ke ikirarin kansu a matsayin shugabannin kungiyar. Shugaban kungiyar na kasa Aimu Foni, shi ya bayyanwa manema labarai ranar Juma’a a Abuja.
Shugaban, ya ce kiran ya zama dole ne don kar a sanya mambobi da sauran jama’a cikin rudani. Aimu Foni ya lura cewa an gudanar da wani haramtaccen zabe da shugabannin kungiyar na asali basu san da shi ba, inda ya kalli lamarin a matsayin wani bangare na kokarin cimma wasu manufofi.
kungiyar a makon da ya gabata ta gudanar da taron zartarwa na kasa na shekara-shekara a Abuja don tsara shirye-shirye na 2021 karkashin Honarabul Aimu Foni.
Ya ci gaba da cewa kungiyar a karkashin jagorancinsa za ta hada kai da ma’aikatar noma da ci gaban karkara ciki har da babban bankin Nijeriya don tabbatar da cewa mambobin sun amfana da shirin na rancen na Anchor. Shugaban kungiyar na kasar, ya tabbatar da cewa daga cikin ajandar taron da suka gabatar a Abuja shi ne batun zabe wanda aka dage saboda barkewar cutar Korona.
Ya jaddada cewa kungiyar ta yanke shawarar gudanar da zabe a Fabrairu, yana mai nuni da cewa wadanda ke gabatar da kansu a matsayin shugabanni suna shirin fuskantar karar da aka shigar da su kotu. Aimu Foni ya ci gaba da cewa, sun kuduri aniyar yin aiki tare da shugabannin gwamnatocin jihohi 36 da sauran masu ruwa da tsaki don farfado da noman gyada mai yawa a Nijeriya.
Tun farko da Honarabul Aimu Foni ya ambata, akwai bukatar su zauna domin sasantawa, saboda yawan zagon kasa a kan shugabanci ba zai kawo musu komai ba, sai dai Haifar da nakasu daga bangaren gwamnati,
Tun farko da Honarabul Aimu Foni ya ambata, akwai bukatar su zauna domin sasantawa, saboda yawan zagon kasa a kan shugabanci ba zai kawo musu komai ba.
Da aka tambayi shugaban ko yaya matsayin zaben da mabobin kungiyar suka gabara a makon da ya gabata? Sai ya ce, “ A’a wannan ba kungiyarmu bace jabu ne karya ne, wadannan masu hanzari ne, akwai dai ‘yan kungiyarmu daya biyu uku a ciki, kuma su din ma ba ‘yan kungiyarmu ne masu rajista ba, ba mu san su ba ba su da wani mukami, amma yau gashi a gabanka dukkan zababbunmu suna zaune, idan da gaskiya ai kyau a ce dukkan wasu zababbu namu suna tattare da su. Kotu fa muka kai, idan idan kuma da wata magana ma to sai dai in kotu ta yi kira, kotu muke ce muke jira ta kira su, kotu ce mu ke jira ta yi aikinta, mu kuma mu je ba da bayananmu.”
Da aka tambaye shi ko ya yake ganin idan har daya bangaren suka nema a zauna a yi sulhu? Sai ya ce to ai ni na kira su, na gaya maka wannan na Neja wanda ake kiransa so col Secretary, na ce masa a’a ka gaya wa BOT dinmu lamarin wannan kungiya tamu yana bukatar mu zauna mu fahimci juna, ba a kai ga fada a je ana cutar talakawa ba, domin da zarar mun yi fada to za a samu matsala ga talakawa kuma hakan bai kamata ba. To amma zan kai batun kotu idan aka samu aka fitar da bayanai ka ga za mu samu fahimtar juna, ai dukkanmu ‘yan Arewa ne. Da aka sake tambayarsa, shin ba ya ganin wannan abu da ya taso, zai iya kawo musu nakasu a bangaren babban bankin Nijeriya wajen neman rancen da kungiyarsu ke yi ga mambobin kungiyar, a wannan lokaci da gwamnati ke yunkurin bunkasa harkar noma ciki kuwa har da noman gyada,?
Fulani Ba ‘Yan Ta’adda Ba Ne –Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce...