Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Wasu masu haya da Babura masu kafa uku a Jihar Kano na yunkurin janyewa tare da tsunduma yajin aiki na jan kunne daga ranar Litinin sakamakon gazawar Gwamnatin Jihar Kano na dakatar da karbar harajin Naira 100 kowacce rana.
A ranar asabar data gabata ne dai masu baburan adaidaita sahun suka fantsama tituna domin sanar da ‘yan uwansu tare da raba masu takardun shirin su na tsunduma yajin aiki tun daga farar safiyar ranar litinin, wannan kuma ya biyo bayan tashi baran baran da akayi a taron da aka gudanar da tsakaninsu da Gwamnatin Jihar Kano da Kungyoyinsu.
Shugaban kungiyar masu Babura masu kafa uku na Jihar Kano Alhaji Sani Dankoli wanda ya tabbatarwa da manema labarai cewa, matuka baburan masu kafa uku sun yanke shawarar shiga yajin aiki ba tare da amincewar kungiyoyinsu ba. Saboda haka sai Dankoli ya bukace su dasu gaggauta janye wannan yajin aiki, inda yace yajin aikin zai shafi zirga zirgar dubban mutane a fadin Jihar Kano.