Masu Amfani Da Internet Sun Kai Miliyan 98 Nijeriya – NCC

Hukumar Sadarwa ta kasa NCC ta bayyana cewa masu amfani da hanyar Sadarwa ta Intranet sun haura mutum Miliyan 98 a kididdigar da aka gudanar zuwa watan Nuwamba na shekarar 2017.

Hukumar ta yi wannan bayanin ne a rahoton ta na wata wata na watan Disamba 2017 da ta wallafa a shafin ta nan internet ranar Alhamis da ya gabata a Abuja.

Rahoton ya nuna cewa, kanfanin sadarwa na Airtel ne a kan gaba yayin da kanfanin Glo ke biye da shi wajen samun yawan masu amfani da internet, kanfanin 9mobile ce bata samu karuwar masu amfani da internet ba ta hanyar ta.

Masu amfani internet sun karu da mutum 98,391,456 a watan Disamba daga mutum 94, 818,553 a watan Nuwamba abin dake nuna karuwar 3, 572,903.

Bayanin ya kuma nuna cewa, kanfanin  MTN ne ta fi samun sabbin masu amfani da internet da mutum  2,642.666 a watan Disamba, sabbin shiga sun kai 36,069,597, daga cikin mutum 33,426,931 da suka shiga a watan Nuwamba.

Kanfanin 9mobile sun yi asarar mutum 68,341 masu amfani da internet a watan Disamba hakan ya dawo da masu hurda da ita zuwa 11,338.839 maimakon 11,407,180 da ta samu a watan Nuwamba.

Kanfanin Airtel ne ta fi samun karuwar da mutum 911,040 sabbin da suka fara amfani da internet a watan Disamba abin da ke nuna mutum 23,985.203 ne suka hau a maimakon 23,074,163 masu amfani da internet a watan Nuwamba shekarar 2017.

Rahoton ya kuma nuna cewa ita ma kanfanin Globacom ta samu karuwar sabbin hannu har 87,538 a watan Disamba in da gaba daya masu hurda da internet din ta ya kai mutum 26,997,817 a watan Disamba maimakon 26,910,279 da aka samu a watan Nuwamba ta 2017.

Exit mobile version