Masu Amfani Da Salula A Nijeriya Sun Kai Miliyan 140 –NCC

Hukumar sadarwa ta Nijeriya, (NCC), ta ce, akwai masu amfani da wayar salula milyan 140, ya zuwa watan Satumba na shekarar 2017.

Mataimakin Shugaban hukumar ta NCC, Farfesa Umar Garba, ne ya bayyana hakan wajen bikin ranar hukumar a kasuwar duniya ta Kaduna, wacce ke ci a yanzun haka.

Ya kuma kara da cewa, ya zuwa wannan lokacin da ake magana, akwai masu amfani da shafukan yanar gizo milyan 92 a wannan kasa tamu.

Mataimakin Shugaban, wanda mataimakiyar Daraktansa, Hajiya Amina Shehu, ta wakilce shi, ya ce, amfani da shafukan zamani na yanar gizo, yana kara habaka ne a kasarnan, inda ya ce, “Jama’anmu suna more damar da aka ba su na yin amfani da shafukan zamani a kasarnan ba tare da kaidi ba.”

Hukumar ta roki masu amfani da shafukan da su kara hakuri da matsalolin da ake fama da su a halin yanzun, kamar yadda ake samun rashin kyawun fitar shafukan, da yanda ake ciran masu kudade bisa kuskure, da kuma yadda ake shigar da su wasu shirye-shiryen da ba su yi niyyan hakan ba.

Ya Bayyana cewa, “Mun sanar da jami’an da muke hulda da su a kan hakan. Ba da jimawa ba, za mu kira su domin su gyara mana.

“Idan kuwa har suka kasa gyara mana, za mu kai kara wajen da ya dace, domin a yi mana hukuncin da ya kamata a tsakaninmu da su.”

Shugaban hukumar ta sadarwa, ya kara tabbatarwa da al’umma cewa, dogayen na’urorin amsa kuwwa, na hukumar sadarwar ba su da wata barazana ga lafiyar su, kamar yadda wasu mutane suke zato.

“Hukumar Sadarwa, ta samu tabbaci daga, Hukumar kula da lafiya ta duniya, (WHO), kan cewa, babu wani sakamakon da ya nu na wani hadarin da ke tattare da iren wadannan na’urorin.

Exit mobile version