Connect with us

KASUWANCI

Masu Amfani Da Waya 16,287 Suka Canza ‘Network’ A watan Yuni – NCC

Published

on

Masu amfani da layukan waya sun canza  wadanda suka samar masu da damar isar da sakonsu, a karkashin Mobile Number Portability (MNP).

Hukumar ce ta bayyana hakan a wani al’amari na kiran ayar da yake shigowa, da kuma wanda ake yi, na rahoton ayyukan kamfanonin sadarwa ta waya, ta suka buga a hanyar sadua ta zamani.

Hukumar ta bayyana cewar daga cikin kiraye kirayen 16,287 na waya wadanda aka yi a watan Yuni na wannan shekarar, 8,142 mau shigowa ne, yayin da kuma 8,145 masu fita ne.

Hakanan ma cikin watan Mayu na wannan shekarar duk daga cikin kamfanonin bada dama ta sadarwa an samu 13,203, wannan kuma ya nuna ke nan an samu karuwa cikin watan Yuni  an samu karuwa , ta 3,064

Kamar  dai yadda Hukumar ta shaida masu amfani da waya 2,474 sun bar layin waya na Airtel zuwa wasu layukka, cikin watan Yuni.

Wadannan alkalumma abin ya nuna an samu karuwa ta 231 daga cikin 2,243 na masu amfani da layin Airtel, adanda suka bar layin cikin watan Mayu.

Hakanan ma ita Hukumar ta kara bayyana cewar suma masu amfani da layin Globacom, cikn watan Yuni ne suma suka bar amfani da layin kamfanin, wannan kuma ya nuna an samu  karuwar 145 akan masu amfani da layin 1,907 wadanda suka bar amfani da layin cikin watan Mayu.

Bugu da kari kuma msu amfani da layin 9mobile suma sun canza akala zuwa amfani da wani layuyyukan duk dai a cikin watan Yuni, wanda kuma na samu karuwa ce ta519 idan aka yi la’akari da masu amfani da layin wadanda suka bari a watan Mayu na wannan shekarar, da suka kai 1,587.

Hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta ce shi ma kamfanin MTN ya rasa masu amfani da layin shi, da suka kai 1,516 a watan Yuni, wannan kuma karuwa ce aka samu ta 546, idan aka yi la’akari da wadanda suke amfani da layin kamfanin 970, adanda suka bar amfani da layin  cikin watan Mayu na wannan shekarar.

Idan kuma ana maganar kiran da yake shigowa kamfanin 9mobilebn shi ne ya zama jagora da karuwar masu amafni da layin cikin watan Yuni, na 3,555 akan network din ta, cikinn watan Yuni.

Bayanin ya kuma nuna cewa, kanmfani 9mobile tayi gaba da karin masu amfani ita har mutum 3,555 a cikin watan Yuni na wannan shekarar.

Kamfanin MTN ceta zama ta biyu da karin masu amfani na ita zuwa mutum 3,243 subscribers yayin da masu amfani da Airtel suka karu da mutum 911 ita kuwa Globacom ta samu karin mutum 433 ne kawai.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: