Masu Amfani Da Yanar Gizo A Duniya Fiye Da Miliyan 26 Sun Tattauna Kan Binciken Ra’ayoyin Jama’a Da CGTN Ta Yi

CGTN

Daga CRI Hausa,

 

Game da batun asalin kwayar cutar COVID-19, kungiyar masana ta CGTN ta yi binciken ra’ayoyin jama’a cikin harsuna shida wato Sinanci, da Turanci, da Spansanci, da Faransanci, da Larabci, da Rashanci a shafukan YouTube, da Twitter, da Facebook da sauransu tare da kaddamar da rahoton binciken, wanda ya jawo hankalin masu amfani da yanar gizo a duniya sosai.

Sakamakon binciken ra’ayoyin jama’a da aka gabatar a ranar 26 ga watan Yuli, ya nuna cewa, kashi 80 cikin dari na masu amfani da yanar gizo a duniya suna ganin cewa, an riga an siyasantar da aikin binciken asalin kwayar cutar COVID-19. Kana sakamakon binciken da aka gabatar a ranar 30 ga watan Yuli, ya nuna cewa, kashi 83.1 cikin dari na masu amfani da yanar gizo a duniya sun amince da a gudanar da binciken a kasar Amurka.

Ya zuwa yanzu, rahotanni game da binciken ra’ayoyin jama’a da kungiyar masana ta CGTN ta yi sun jawo hankalin masu amfani da yanar gizo a duniya fiye da miliyan 26, kana masu amfani da yanar gizo a duniya fiye da dubu 280 sun bayyana ra’ayoyinsu cikin harsuna daban daban, inda suke ganin cewa, ya kamata a gudanar da aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19 a sassan daban daban na duniya.

Wani mai amfani da yanar gizo mai suna Harmony Voice, ya bayyana ra’ayinsa a kan shafin yanar gizo cewa, ya kamata hukumar WHO ta duba yiwuwar gudanar da bincike a dakin gwaje-gwaje na Fort Detrick na kasar Amurka a nan gaba. Amma kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya ba su ambaci wannan daki ba.

Bisa binciken da aka yi, an gano cewa, an fi yin amfani da kalmomi kamar matsin lamba na siyasa, da takunkumin da Amurka ta sanya, da hana bunkasuwar kasar Sin a cikin ra’ayoyin da masu amfani da yanar gizo suka bayyana. Koda yake masu amfani da yanar gizo sun fito ne daga sassa daban daban na duniya, amma ra’ayoyin da suka bayyana a yayin binciken jin ra’ayoyin kusan iri daya ne, inda suka yi amfani da harsuna daban daban don bayyana ra’ayi iri daya. (Zainab)

Exit mobile version