Connect with us

KASUWANCI

Masu Biredi Sun Yi Maraba Da Fulawar Dangote

Published

on

Masu yin Burodi a kasar nan, sunyi na’am da sabuwar Fulawar da Kamfanin rukunonin Dangote dake sarrafa Fulawa, India suka danganta Fulawar a matsayin mai kyau kuma mai inganci.

Yabawar tana kunshe be a aikin sanarwar da Kamfanin ya fitar, inda aka jiyo masu gidan Burodin suna cewa sabuwar Fulawar tanada saukin saya akan yadda ake sarrafa Burudi kuma zasu iya samun riba sosai.

Snarawar taci gaba da cewar, kimanin masu gidan Burodi  80 aka gayyata zuwa wani gidan Burudi, inda aka sarrafa Burodi da sabuwar Fulawari don yin gwaji akantai yadda sakamakon ya nuna cewar, tafi wadda take kasuwa samun riba in an sarrafa Burodi.

Shugaban kungiyar masu gidan Burudi reshen jihar Kano Alhaji Muazu Gidauniya,

aji Muazu Gidauniya, sanarwar ta ruwaito yana cewa, yaji dadi sosai da zuwan sabuwar Fulawar kuma wasu yayan kungiyar suma sunyi gwajin Fulawar a gidajen Burudinsu kuma sabuwar Fulawar baza’a iya yi mata gauraye da tsohuwar Fulawar da tuni take a kasuwa ba kuma wadda aka share shekaru, ana yin amfani da ita.

Mai rabar da Fulawar Dangote a Bihar Kano kuma Sakatare Janar na kungiyar masu gidan Burodi Kabiru Abdullahi, shi ma ya nuna jin dadinsa da sabuwar Fulawar, Inda yace zata samu kasuwa sosai a kasuwa.

Har ika yau, sanarwar ta kuma ruwaito Babban Darakta ta sashen kasuwaci ta Kamfanin Haluma Dangote ta ce, sabuwar Fulawar tanada inganci da samar da riba kuma anyi tane, da Alkama mai inganci da za’a iya yin amfani da ita naga sarrafa Burodi ba kawai harda sauran abinci.

Kamfanin ya kuma kaddamar da wani sabon shiri mai suna a turance, ‘My own don bbeta inda diloli zasu iya cin gasar wasu farashi.

Shi ma Manajan saye da sayarwa na shiyya  Nura Rabo ya nuna jin dadinsa a bisa samar da sabuwar Fulawar.
Advertisement

labarai