Masu Fama Da Sikila A Bauchi Sun Bukaci A Kafa Hukumar Kula Da Su Ta Musamman

Sikila

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Masu fama da cutar Sikili a Jihar Bauchi sun roki gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari, da ta taimaka wajen ceto rayuwar masu dauke da cutar Sikila sama da miliyan 40 da ke tagayyara gami da mutuwa sakamakon jinyar cutar a fadin kasar nan.

Haka zalika, majinyatan sun nemi gwamnatin Jihar da ta kafa wata hukuma mai zaman kanta da za ta ke kula da harkokin rayuwar masu dauke da cutar, domin ganin an rage musu radadin rayuwa da suke fama da su tare da yin doka da za ta tabbatar da ana yin gwajin kwayar hallitta kafin aure domin rage yawan masu dauke da cutar a jihar da ma kasar nan.

Shugaban wata kungiyar masu fama da cutar Sikila gami da neman agaji da tallafa wa masu cutar wato ‘Sickle Cell Aid Foundation Bauchi’, Malam Muhammad Kafi Liman shi ne ya yi wannan kiran a ganawarsa da wakilinmu dangane da bikin tunawa da ranar masu fama da cutar Sikila ta Duniya da aka gudanar a shekaran jiya a fadin duniya.

Masu fama da cutar sun bayyana sayen magunan yau da gobe tare da yunwa gami da zazzabin cizon sauro, kyama da tsangwama musamman a fannin neman aure a matsayin manyan matsalolin da suke addabarsu wadanda suke neman hukumomi su kawo musu dauki cikin gaggawa.

 

Liman ya ce, “Sama da yara 300,000 ake haifa dauke da cutar Sikila duk shekara, sama da mutum miliyan 40 ne kididdiga ta nuna suna dauke da cutar a fadin kasar nan.”

Shugaban kungiyar ya kuma bayyana cewar mutum 150, 000 ke rayuwa da wannan cutar ta Sikila a Jihar Bauchi wadanda suke neman agajin gwamnatin Bala Muhammad.

 

Sannan kungiyar sun nemi gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad da ya yi kokarin magance musu annobar zazzabin cizon sauro tare da samar da tsaftar muhalli a fadin Jihar Bauchi.

Shugaban kungiyar ya nemi gwamnatin Bauchi da ta kafa wata hukuma mai cin kashin kanta domin saukaka kula da jinyar masu cutar Sikila don ganin suna samun magunguna kyauta ko cikin sauki tare da samar musu da magungunan sha na yau da gobe.

Ya ci gaba da cewa, “Masana da kididdiga ya nuna cewa ana haifar sama da mutane 5,000 masu cutar Sikila duk shekara ban da adadin da muke da su a yanzu haka, fiye da 2,100 suna mutuwa a take, 2,900 suna rayuwa cikin matsanan cin hali sakamakon gazawar. Gwamnatin shugaba Bala Muhammad Abdulkadir na rashin kafa dokar tilasta yin gwajin kwayoyin halittar mutane kafin Aure a fadin jiha.

“Sama da mutane 800 ne suke mutuwa duk shekara sakamakon rashin kulawar Gwamnatin shugaba Muhammad Abdulkadir (Kauran Bauchi) akan majinyatan na rashin samar da tallafin magunguna tare da kayan abinci masu gina jiki.”

“Muna amfani da wannan rana ta tunawa da masu dauke da cutar Sikila ta duniya don isar da kokenmu ga Gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin mai girma Gwamnan Bala Muhammad Abdulkadir da ya taimakemu ya kawar mana da damuwoyinmu, wadanda suka fi addabar ‘yan uwanmu masu cutar Sikila a fadin jihar.

“Ita wannan zazzabin na cizon sauro ita kadai ta kan dauki kashi 50 na azabar da masu cutar Sikila suke ciki, musamman ta yadda zazzabin cizon sauron yake haddasa mana yawan karin jini ta bangaren karancin jini.

“Sannan muna bukatar Gwamnan da ya samar mana da magungunan zazzabin cizon sauro, ragar kwanciya tare da kayan feshin kwari, ya kasance kyauta ga masu cutar sikilar, tare da samar da ingantaccen tsaftar muhalli wanda shi ne kashin bayan yaki da zazzabin cizon sauron.

 

“Na biyu, muna rokon gwamnatinta samar mana da kayan abinci mai gina jiki tare da sassauta tsadar farashin kayan abincin ga masu dauke da irin wannan cutar domin abinci mai gina jikin na taimaka wa yanayin jikinmu.”

 

Kungiyar ta kuma nemi gwamnatoci da su tabbatar da kafa dokar yin gwajin kwayar halitta kafin aure domin guje wa yaduwar cutar sikila da ke tagayyara yara da jefa su cikin ukubar rayuwa.

 

Liman ya nemi gwamnatin Bala Muhammad da ta sauran jihohin kasar nan da su kafa wata hukumar kare hakkin masu cutar Sikila don rage yawan cin zarafinsu, kyama da tsangwama da suke gani.

 

“Gwamna muna rokonka ka taimaka mana ka haramta kai wa masu cutar Sikila makarantun Allo ta yadda malaman suke gallazawa ‘yan uwan mu, musamman a cikin kauyuka da birane don ganin su ma iyayensu sun gaji da dawainiyar su.

 

“Fatanmu gwamnatinka ta samar wa masu cutar Sikila ingantacciyar hanyar dogaro da kai mai inganci, ta yadda za mu rika dogaro da kanmu bisa la’akari da irin azabar rayuwa da muke ciki.

 

“Tare da samarwa hanyar da za a daina kyamar majinyatan sikila ta kowanne fanni, musamman ta bangaren Auratayya. Dubban ‘yan mata da daidaikun samari muna fuskantar wulakanci da kyama a fannin auratayya duk lokacin da muka je neman aure.

“Samari na gudun auren mata masu Sikila tamkar yadda suke gudun talauci saboda tunanin wahalar dawainiyar faman zuwa asibiti don kula da lafiya da magungunan amfani yau da kullum.”

Har-ila-yau, Muhammad Kafi Liman, ya roki kungiyoyin kasashen waje da su ma su taimaka wa masu mafa da cutar sikila a Nijeriya lura da halin da suke ciki, yana mai nuna korafinsu kan cewa a wasu cutukan kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje da dama suna mai da hankalinsu tare da samar da tallafi, amma sun yi biris da masu cutar Sikila duk kuwa da cewa sun ma fi shan wahalar rayuwa.

 

 

Exit mobile version