Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Masu Fitar Da Kayyaki Sun Bukaci Gwamnati Ta Tallafa Mu Su

Published

on

Masu gudanar da kasuwancin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tallafa wa harkokin kasuwancisu, wanda ya tabarbare sakamakon barkewar cutar Korona a kasashen Duniya.

Shugaban kungiyar masu gudanar da kasuwancin fitar da kayayyakin zuwa kasashen ketare, Mista Jayeola Olarewaju, ya bayyana cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta samar da gagarumar shirye-shirye wajen farfado da harkokin  kasuwancin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare wanda ya durkushe sakamakon cutar Korona. Ya gudanar da wannan bayani ne a jiya sannan ya gabatar da hujjojinsa da kuma bukatar tallafa wa kasuwancin fitar da kayayyaki da wasu manufofi domin tallafa wa kasuwancin.

Ya ce, “a halin yanzu ba mu bukatar wani sabon abu ko kuma wani abubuwa wadanda ba su dace ba. Mu na fatan za a fahimmace mu a  kan abubuwan da mu ke bukata a yanzu haka. Mu na bukatan a amince da alkawarukan da aka yi mana tun a watan Disambar shekarar 2018, wajen amince wa da bai wa basussukan ga masu kasuwancin fitar da kayyakin zuwa kasashen ketare wanda ka yi alkawarin za a saka a cikin kasafin kudi, amma har zuwa shekarar 2020 ba a amince a saka wannan bukata ba a cikin kasafin kudi, mun gudanar da taro da kwamitin gudanarwa, amma har yanzu lamarin ya ci tura.”

Olarewaju ya ci gaba da cewa, ya zama wajibi ga gwamnatin tarayya ta farfado da dukkanin fannonin tattalin arziki, domin rage dogaro da man fetur wanda farashinsa ya karye sakamakon barkewar cutar Korona a kasashen Duniya. Ya kara da cewa, gwamnatocin kasashen Duniya sun fara samar da wasu hanyoyin farfado da tattalin arziki, domin tallafa wa rayukan ‘yan kasa.

Masu kasawancin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare sun fadakar da gwamnatin tarayya na yadda kasar China ta mayar da hankali wajen gudanar da harkokin kasuwanci.

Sun bukaci gwamnati da ta rage yawan harajin da take kakaba musu wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare a kan kowani kayayyaki da ya kai yawan 1500, ta yadda zai kara mu su kwarin gwiwa wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu yadda ya kamata.

Sun ci gaba da cewa, taimaka wa masu gudanar da kasuwancin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare zai bai wa gwamnati tarayya damar samun gagarumar kudaden haraji da  bunkasa tattalin arziki a hannu daya kuma. Sun ce, suna kira ga wannan gwamnati da take kokarin farfado da tattalin arzikin kasar nan a dai-dai wannan lokaci, akwai bukatar inganta harkokin noma da farfado da masana’antu, domin bunkasar tattalin arziki mai daurewa tare da rage dogaro da fannin man fetur wanda darajansa ya ke kara yin kasa a kasuwannin Duniya.

Masu kasawancin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare sun ce, idan gwamnati ta bi wadannan hanyoyin da su ka lissato, to za su sami damar gudanar da kasuwancinsu cikin sauki ba tare da wani shan wahala ba, sannan za a iya farfado da rayuwar mutane da dama.

Sun ce, su na fatan gwamnatin tarayya za ta ci wannan kuka nasu ta tallafa mu su, domin gudanar da kasuwancinsu yadda ya  kamata a ko’ina a fadin Duniya.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: