Masu Garkuwa Da Mutane Da Barayin Motoci Sun Shiga Hannu A Kebbi

Rundunar ‘yan sandan jihar kebbi ta samu nasarar cafke masu laifi goma shadaya da ke garkuwa da mutane da kuma shugaban barayin satar mota a jihar ta kebbi a jiya a Birnin-kebbi.
Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar ta Kebbi , CP Ibrahim Kabiru ne ya bayyana hakan ga manema labaru a ofishinsa da ke helkwatar rundunar ta ‘yan sanda da ke a Birnin-Kebbi a jiya, cewa wannan nasarar cafke masu laifin yana daya daga cikin matakai da rundunar ta dauka domin tabbatar da cewa jihar kebbi ta samu kyakyawan tsaro.
Ya ci gaba da cewa, a cikin watan Yuli na wannan shekara rundanar tayi nasarar cafke masu garkuwa da mutane goma shadaya kuma tuni an kammal bincikensu har an gabatar dasu a gaban kotu domin yi musu hukuncin da dokar kasa ta tana da. Haka kuma ta cafke gungun masu satar mashin din achaba a jihar ta Kebbi wanda Malam Zaki Mamman shi ne shugabansu ga sace-sacen mashin a cikin jihar. Haka kuma yace, suma masu satar motoci a cikin jihar ta Kebbi an samu nasarar cafke Mista Peter James a matsayin shugaban barayin satar motoci a jihar wanda bada bata lokaci ba za’a gabatar dashi a gaban kotu”, Inji kwamishinan rundunar .
Har ilayau yace” ofishin rundunar ya fito da wani sabon mataki da zata yi aiki dashi domin tabbatar da cewa ta magance matsalar aikata miyagun laifufukka a jihar ta kebbi kamar yadda kididiga ta nuna cewa jihar kebbi tafi kowace jihar a kasar nan karancin aikata miyagun laifufukka”. Haka kuma yace “ kawo yanzu rundunar ta cafke masu laifi 291 kama daga cikin laifin akwai masu garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma satar shanu duk a cikin jihar. Amma kuma wurin gudanar da bincike mutanen 44 an sakesu domin bincike ya nuna cewa basu da wani laifi da yakamata su amsa kan abin da ake tuhumar su da aikatawa.
Bugu da kari kwamishina Ibrahim Kabiru yace” cikin masu laifi 291 da aka kama 224 tuni an gabatar dasu a gaban kotu wanda kuma 201 kotu ta yanke musu hukunci, sai kuma laifi 17 na jiran hukuncin kotu” . Ya kuma ja hankali jama’ar jihar ta kebbi kan yin kasuwaci da mutane ta yanar giro cewa suyi hattara domin akwai mayaudara da kuma barayi ga irin wannan kasuwancin , saboda haka ya yi kira dasu kula.
Daga nan kwamishinan ya yi kira ga jama’ar jihar kebbi dasu ci gaba da taimakawa rundunar ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro da basu bayanan sirri domin kara samun nasarar cafke masu aikata laifufukka a cikin jihar, ya kuma godewa jama’ar jihar kan irin goyun bayan da ake baiwa rundunar ta ‘yan sanda a jihar kan gudanar da ayyukkan su . Haka kuma ya yabawa ‘yan jaridun a jihar ta kebbi kan irin fahimata ta aiki da ke akwai tsakanin rundunar da kuma ‘yan jaridun masu aiki a cikin jihar domin duk nasarar da rundunar ta samu da hannun ‘ yan jaridun ne.

Exit mobile version