Connect with us

MANYAN LABARAI

Masu Garkuwa Sun Bukaci Diyyar Miliyan 100 Kafin Su Saki Wasu Mutum Bakwai A Zamfara

Published

on

Jami’an ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara sun ce masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya miliyan 100 a matsayin kudin fansa, kafin su saki wasu mutum bakwai da suka sace a kauyen Nahuce da ke karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Cikin mutanen da aka yi garkuwa da su harda wani tsohon kansila mai suna Bello Daniya, da sanyin safiyar yau masu garkuwan suka yi awon gaba da mutanen.

Shaidun gani sa ido sunce barayin sun yi wa kauyen na Nahuce kawanya, suka yi ta harbe-harbe a sama, sannan suka bukaci jama’ar kauyen da su nuna musu gidan shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Bungudu, wato Alhaji Hamisu Coordinator.

Amma ba su yi sa’ar samun gidan shugaban jam’iyyar ba, sai suka afka gidan kansilan kauyen, wanda makucin shugaban jam’iyyar ne, inda suka sace shi tare da wasu yara maza hudu da mata biyu.

Daga baya sun saki daya cikin yaran, sun bashi sako, inda a cikin sakon suka bukaci a biya miliyan 100 kafin su saki wadanda suke garkuwa da su din, zuwa yanzu jami’an ‘yan sanda sun fara binciken lamarin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: