Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu satar jama’a ne sun yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukumar Olamaboro dake jihar Kogi, Barista Emmanuel Isaac Ekpa a yankin Ochadamu da ke karamar hukumar Ofu da ke jihar.
Irin wannan lamari ya auku a makon jiya, inda wasu yan bindiga suka yi awon gaba da mai rikon mukamin Sarkin Ankpa dake jihar ta Kogi,( Ejeh) Alhaji Shaibu Usman a ya yin da yake kan hanyarsa ta zuwa masallaci don yin sallar Asuba.
Masu garkuwa da mutanen sun samu nasarar sace Sarkin na Ankpa mai daraja ta daya ne da misalin karfe 5.30 na safe gab da fara sallar ta Asuba a ranan juma’a wadda a wannan rana ce masu garkuwa da mutanen suka saci tsohon shugaban karamar hukumar Olamaboro a yankin Ochadamu dake karamar hukumar Ofu akan hanyarsa ta zuwa garinsu,kamar yadda wakilin jaridar LEADERSHIP Ayau ya nakalto.
An ce Ekpa yana shirye-shiryen bikin binne mahaifinsa ne kafin wannan ifti’lai ta fada kansa.
Wakilin LEADERSHIP Ayau ya tuntubi kakakin rundunar yan sandar jihar Kogi, Mista Williams Ayah, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin,yana mai cewa tawagar yan sanda dake yankin Ofu sun gano wata mota da babu kowa a cikntai a kan hanyar Ochadamu.
Ya ce bayan sun yi bincike cikin motar ne,sai suka gano ID card mai dauke da sunan Emmanuel Isaac Ekpa, alamun dake nuna cewa lallai yan bindiga sun yi garkuwa da shi.
Kakakin rundunar ya ce a yanzu haka, kwamishinan yan sansan jihar Kogi, CP Ayuba Edeh ya umurci rundunar yan sanda dasu shiga faraurar masu garkuwa da mutanen tare da tabbatar da ganin sun kubutar da Barista Emmanuel Isaac Ekpa.